Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Yaki Da Kera Makamin Nukiliya Ya Sami Lambar Yabo


Shirin yaki da kera makaman nukiliya na kasa da kasa ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2017 a yau Juma’a.

Mun kasance a cikin duniyar da take fama da baraanar makaman nukiliya fiye da shekarun baya a cewar sanarwar shugaban komitin wannan shirin kyauta ta kasar Norway Berit Reiss-Anderson game da kyautar.

Wannan kyautar zaman lafiyar ta zo ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump yake yiwa Iran da Korea ta Arewa barazana game da makamansu na nukiliya.

Shugaban na Amurka bai yi na’am da yarjejeniyar makamin nukiliya ta Iran ba, matakin da ya kira mafi muni da aka taba dauka. A cikin wannan lokaci Trump ya bayyana ra’ayinsa a babban taron Majalisar dinkin duniya cewa zai yi amfani da karfin soja ya yi kaca kaca da Korea ta Arewa saboda shirinta na makaman nukiliya.

Duniya na cikin tsananin rudu, lokacin da ake cacar baki mai tsananin zafi da ka iya kaimu ga wani al’amari mai muni da ba zato ba tsammani.

Kwamitin shirin kyautar Nobel yace ya ayyana shirin yaki da kera makaman nukiliya wanda ya ci kyautar ne, saboda rawar gani da yake takawa wurin fadakar da al’umma a kan mummunan lahani da makaman nukiliya ke yiwa bil adama da kuma nasarar da shirin yayi wurin kulla yarjejeniyar hana kera irin wadannan makaman.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG