Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Duniya Sun Ce Alassane Ouattara Ne Zababben Shugaban Ivory Coast


Sojojin Ivory Coast su na gadin hedkwatar hukumar zabe a Abdijan ranar 1 Disamba, 2010.
Sojojin Ivory Coast su na gadin hedkwatar hukumar zabe a Abdijan ranar 1 Disamba, 2010.

Barack Obama na Amurka da Nicolas Sarkozy na Faransa da Ban Ki-moon na Majalisar Dinkin Duniya duk sun ce shugaban hamayyar ne ya lashe zaben shugaban kasa, sun kuma nemi da Laurent Gbagbo ya mutunta wannan sakamako

Shugabannin kasashen duniya sun bayyana goyon bayansu ga shugaban hamayya na kasar Ivory Coast ko Cote D’Ivoire, Alassane Ouattara, a zaman wanda ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa, inda suka yi watsi da wani sabon sakamakon da aka yi ma kwaskwarima dake nuna cewa Laurent Gbagbo ne ya lashe zaben.

Shugaban Amurka Barack Obama, da shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa, da kuma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, duk sun bayyana cewa Alassane Ouattara ne zababben shugaban kasar Ivory Coast, sun kuma yi kira ga Mr. Gbagbo da ya amince da sakamakon zaben na gaskiya.

Jiya jumma’a majalisar tsarin mulki ta Ivory Coast ta soke sakamakon da hukumar zabe ta bayar dake cewa Ouattara ne ya lashe zaben shugaba, ta bai wa Mr. Gbagbo nasara.

Da asubahin yau asabar, gidan telebijin na gwamnatin Ivory Coast yace sojojin kasar sun bayyana biyayyarsu ga Mr. Gbagbo, ya kuma ce nan gaba a yau za a rantsar da shi.

Shugaban majalisar tsarin mulki, Paul Yao N’Dre, yace sun soke zabe daga wasu yankuna bakwai na arewacin kasar, inda Ouattara yake da farin jini sosai, a bayan da wai suka gano cewa an yi magudi. Shi dai shugaban wannan majalisa na hannun damar Mr. Gbagbo ne.

Wani matashi yana jefa taya cikinw uta a bayan da magoya bayan Alassane Ouattara suka fara zanga-zangar nuna kyamar kwace masa nasarar da suka ce ake kokarin yi
Wani matashi yana jefa taya cikinw uta a bayan da magoya bayan Alassane Ouattara suka fara zanga-zangar nuna kyamar kwace masa nasarar da suka ce ake kokarin yi

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Ivory Coast, Choi Young-jin, ya kira taron ‘yan jarida jiya jumma’a a Abidjan inda yayi Allah wadarai da sabon sakamakon da majalisar ta bayar, abinda ya sa har wani babban mashawarcin Mr. Gbagbo yayi barazanar cewa za a kori wakilin na majalisar dinkin duniya daga kasar.

Shi ma Alassane Ouattara ya yi watsi da sabon sakamakon, ya kuma ayyana kansa a zaman zababben shugaban kasa.

Ana kyautata zaton cewa abinda majalisar tsarin mulkin ta yi zai kara lalata lamarin tsaro a kasar. Tashin hankalin siyasa ya riga ya kashe mutane akalla 14.

XS
SM
MD
LG