Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kudu Za Ta Haramta Amfani Da Kudaden Kasashen Waje


Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Kasar Sudan Ta Kudu Salva Kiir

Sudan Ta Kudu za ta haramta amfani da kudaden kasashen waje a kasar, a zaman hanyar magancen tabarbarewar tattalin arziki da tashin farashin kayan masarufi.

Babban Bankin kasar Sudan ta Kudu ya ce yana shirin haramta amfani da kudaden kasashen waje a duk fadin kasar, domin kaucewa kara tabarbarewar darajar kudin kasar na pound akan dalar Amurka.

Wannan dai ya biyo ne bayan tashin gwauron zabi da kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi suka yi a kasar a ‘yan watannin nan.

Wata mazauniya garin Juba, Saida Juan, ta ce a duk lokacin da ta tafi kasuwa, sai ta tarar farashin kayayyaki ya kara tashi. Akan haka ta yi kira ga jami’an gwamnati, da su yi duk abin da ya kamata domin daidaita farashin.

Ta ce “’yan kasuwa da ke sayar da kayayyaki suna dora alhakin tashin farashin ne da karin canjin dalar Amurka a kudin pound na Sudan. Kira na ga shugabanni shi ne su yi kokarin hana kudaden kasashen waje suna mamaye kasuwanninmu domin dala ba kudinmu ba ne. Hakika muna shan wuya sosai.”

A ranar Alhamis, kwamitin sha’anin kasuwanci na majalisar dokokin Sudan ta Kudu, ya gayyaci gwamnan babban bankin kasar Gamal Abdallah Wani, da Ministan Kudi Garang Mabior da kuma mataimakin kwamishinan hukumar tara haraji ta kasa Erjok Bullen, domin su amsa tambayoyi akan faduwar darajar kudin kasar na pound.

Gwamnan Babban Bankin Sudan Ta Kudu Gamal Abdallah Wani tare da Tsohon Shugaban IMF
Gwamnan Babban Bankin Sudan Ta Kudu Gamal Abdallah Wani tare da Tsohon Shugaban IMF

Wani ya fadawa kwamitin cewa Babban Bankin na Sudan ta Kudu, zai kafa sabuwar dokar haramta amfani da kudaden kasashen waje, ya kara da cewa “kowa na yawo da kudaden kasashen waje barkatai ba bisa ka’ida ba a kasar.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG