Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitacciyar Ziyarar Zarif A Faransa Ya Dauke Hankali A Wurin Taron G7


Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif

Babban jami’in diflomasiyyar Iran, ministan harkokin waje, Mohammad Javad Zarif, ya bayyana jiya Lahadi a garin da ake gudanar da taron G-7 na Shugabannin manyan kasashen duniya, amma bai gana da jami’an Amurka ba a lokacin da ya kai wannan takaitacciyar ziyarar.

Sai dai bayyanar Zarif a Biarritz, inda shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ta ganawa da shugabannin wasu kasashe shida, yazo da mamaki.

A lokacin da aka tambaye shi akan ci gaba da aka samu Trump ya ki ya ce komai.

Amma ziyarar Zarif ta zo ne a bisa gayyatar Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, wanda ya tattauna tare da takwaran aikinsa na Iran, Hassan Rouhani, akan zaman dar-dar din da ake yi a yankin tekun Pasha, wanda ke da alaka da janyewar da Trump ta yi bara daga yarjejeniyar kasa-da-kasa ta 2015 da aka cimma da zummar hana Tehran ayyukan kera makan nukiliya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG