Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Yi Kaca Kaca Da Tungar Sojojin Afghanistan


Afghanistan

Hukumomi a kudancin Afghanistan sun fada a yau Asabar cewa sadarwa ta yanke tsakaninsu da wasu sojoji biyo bayan wani samame da kungiyar Taliban ta kai a wata tungar soji a lardin Uruzgan.

Mai magana da yawun rundunar sojojin Afghanistan ya fadawa Muryar Amurka cewa wata mummunar fada ta barke, biyo bayan mummunar harin da 'yan ta’addan suka kai a gundumar Chinarto

Kanal Yahaya Olawee yace a na ci gaba da gwabza fada a wurare da dama, amma dai zai yi karin bayani nan gaba.

A lokacin dabam dabam, babban 'yan sandan gundumar ya fadawa Muryar Amurka cewa sojoji dari na dakarun Afghanistan ne aka jibgesu a tungar, amma yanzu haka ba a san inda suke ba, bayan harin da Taliban ta kai a wurin. Akhtar Mohammad ya kyautata zaton sojojin sun bada kai ne ga 'yan ta’addan, kuma ya tabbatar da 'yan ta’addan sun rusa tungar sojin.

Wani kakain 'yan ta’addan Qari Yousaf Ahmadi, yace wadannan manyan hare haren Taliban ta kai, sun yi kaca kaca da tungar dakarun Afghanistan kuma sun kashe sojoji 55 kana suka kama wasu guda shida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG