Accessibility links

Taron Neman Zaman Lafiya A Filato


Taron shugabannin addinai kan zaman lafiya a jihar Plateau, Nigeria

Shugabannin addini da na al'umma sun yi taron neman zaman lafiya a Yelwa Shendam

Shugabannin addinan Krista da Musulunci da ma na al'umma sun dukufa kain da nain domin tabbatar da dawamamman zaman lafiya a Yalwa cikin karamar hukumar Shendam ta jihar Filato.

A shekarun baya dai Yelwa Shendam ta yi kamarin suna game da tashe-tashen hankali da suka yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa da kadarori yayin da jama'a da dama suka tsere daga garin.

Ranar Asabar da ta gabata darikar Katolika ta shirya wani taro a mijami'arta wanda ta samu halartar dimbin musulmai tare da kiristoci.Rabaran Fada Makel Kelong ya yi murnar ganin yadda musulmai suka halarci taron tun da safe har zuwa karfe uku. Ya ce sun hada kai da fastoci da malaman Musulunci domin su wayar da kawunan matasansu a dena tashin hankali.

Wani abun mamaki shi ne yadda musulmai suka gudanar da sallah a harabar mijami'ar ba tare da wata tsangwama ba.Mohammed Awal Ahmad na'ibin masallacin dake hanyar Ibi ya ce su da kiristoci sun hada kai kuma gwamnati ta taimakesu da jami'an tsaro. Ya ce sukan yi taro da malaman addinai na wayar da kawunan matasa domin su tabbatar da zaman lafiya. Wani limamin kirista shi ma ya ce hadin kansu shi ne ya kawo zaman lafiya.

Fada Kelong shi ne ya kafa kungiyar zaman lafiya tsakanin kirista da musulmai da al'umma shekaru uku da suka wuce. Shi ne kuma shugaban kungiyar.

Zainab Babaji nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG