Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Shirin Tattaunawarsu Da Kim Jong Un Na Nan Daram


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

Fadar White House ta ce mambobin gwamnatin Amurka suna kan shirye-shirye game da yadda ganawar Amurka da Korea ta Arewa za ta gudana, bayan da shugaba Trump ya ba da tabbacin cewa taron zai wakana.

Ganawar da aka tsara za a yi a ranar 12 ga watan Yuni tsakanin Amurka da Korea ta Arewa a Singapore na nan daram, a cewar shugaban Amurka Donald Trump.

Trump ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa a daren jiya Asabar.

Shugaban na Amurka ya kara da cewa, mutane sun zura ido su ga ko ganawar za ta kankama, yana mai cewa idan aka cimma matsaya kan kwance damarar makamin nukiliyan na Korea ta Arewa, hakan zai taimakawa yankin na Korea da ita kanta Korea ta Arewa da makwabciyarta ta Kudu da Japan da Amurka da China da ma Duniya baki daya.

A can Korea ta Arewan, kafofin yada labaran kasar a jiya Asabar sun ruwaito cewa, himmatuwar da shugaban kasar Kim Jong Un ya yi kan batun ne, ya sa wannan zama zai kankama.

Shugaban Korea ta Kudu, Moon Jae-in ya gana da takwaran aikinsa na arewa Kim Jong Un, a kan iyakar kasashen biyu mai dauke da dumbin dakaru, inda suka tattauna kan yadda ganawar da Amurka za ta gudana.

Wannan sabon babi na maido da tattaunawar na zuwa ne, bayan da shugaba Trump ya soke ganawar ta Singapore a ranar Alhamis, amma kuma ya sake sauya ra’ayinsa kasa da sa’oi 24.

“Suna so a cimma sabuwar matsaya mai dorewa, idan suka yi hakan, ni a shirye nake tsaf.” Trump ya ce a ranar Juma'a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG