Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya bayyana Sunan Sabon Shugaban Ma'aikatan Ofishinsa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donal Trump ya kawo karshen cece-kuce a kan batun daukar sabon shugaban ma’aikatan ofishinsa, inda ya ambato sunan shugaban hukumar kasafin kudin kasar a matsayin shugaban ma’ikatansa mai riko wanda zai maye gurbin tsohon jami’in sojin ruwa mai ritaya John Kelly.

Da yammacin jiya Juma’a ne shugaban ya aike da wani sakon Twitter yana mai cewa, ina farin cikin bayyanar da darektan hukumar kasafin kudi Mick Mulvany a matsayin shugaban ma’aikatan ofishina mai riko wanda ke maye gurbin John Kelly da ya yiwa kasa bauta da gaskiya.

Mulvany tsohon dan majalisar tarayya na Republican mai wakiltan Carolina ta Kudu da ya yi fice a harkokin tattalin kudi, ya kuma taba rike mukamin shugaban hukumar kare kudaden jama’a, wanda ya ajiye aikin daga bisani.

Mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ta White House yana da muhimmanci da kima, ganin cewa shine mukamin dake kula madaukakin ofishin kasar kana kuma shine mai kula da ainihin ofishin da shugaban kasar Amurka ke zama a ciki na Oval Office.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG