Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Will Smith Ya Mari Chris Rock A Taron Oscars Bayan Ya Fadi Wani Abun Ban Dariya Game Da Matarsa Da Nufin Raha


OSCAR: Will Smith lokacin da mari Chris Rock
OSCAR: Will Smith lokacin da mari Chris Rock

"Kare bakinka daga kiran sunan matata," abin da Smith ya fadi kenan biyo bayan sabanin da ya kai ga mari.

A daya daga cikin lokuta masu ban mamaki a tarihin taron Oscars, Will Smith ya haye kan dakali ya mari mai gabatarwa Chris Rock saboda wani kalami na wasa da ya yi game da matar Smith, Jada Pinkett Smith.

Lamarin ya faru ne yayin da Rock ke gabatar da shirye-shirye yayin bikin 2022. Rock ya fadi wani abun dariya da nufin raha game da Pinkett Smith inda ya ce ta na shirin yin wani fim mai suna ga GI. Jane – ya fadi hakan ne saboda askin kai da ta yi. (Pinkett Smith kuwa ta sha fadi cewa asarar gashin da ta yi, na da alaka da cutar alopecia.)

"Jada, ina son ki," in ji Rock. "Fim din G.I. Jane 2 na nan na jiran ki. Kin ji ko?"

Smith yayi dariya amma da ganin fuskarsa, bai ji dadin maganar ba.

Jin rashin amincewa daga taron, Rock ya ci gaba da cewa, "Wannan abu ne mai kyau!"

A lokacin ne Smith ya miƙe, ya haye kan dakalin ya mari Rock a kumatu.

Yayin da Smith ya koma wurin zama, Rock ya dinga mamaki har da cewa, “Kai, wow… Will Smith ya mare ni.”

"Ka kiyaye sunan matata daga bakin ka!" abin da Smith ya sake fadi kenan.

Bayan girgizar da yayi, Rock ya ɗan dakata na ɗan lokaci sannan ya gaya wa taron cewa: "Wannan dare ne mafi girma a tarihin talabijin"

Amma a wani yanayi mai ban mamaki, sai Smith ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na King Richard - nasararsa ta farko ta Oscars din - kuma ya sake komawa kan dakalin.

Yayin da arangamar da farko ta ma mutane mamaki, duk wani shakku ya goge lokacin da Smith ya yi amfani da lokacinsa na magana a bainar jama'a don neman afuwar abun da ya aikata.

Smith ya share hawaye inda ya ci gaba da cewa: “Na sani, a irin wannan aikin na mu, dole mu daure da cin zarafi. Dole ku kyale mutane su yi magana game da ku. A cikin wannan sana'ar, dole ne ku ba mutane damar su raina ku kuma ku yi murmushi kamar bai dame ku ba. Denzel ya ce da ni 'A lokacin mafi girman irin wannan, ku yi hankali, lokaci ne da shaidan ya ke zuwa muku.'

Ya ci gaba da cewa, “Ina so in nemi gafarar Oscars, ina so in nemi afuwar ga duk wadanda aka zaba. Wannan kyakkyawan lokacin ne, kuma kuka na ke yi ba don samun lambar yabo ba. Ba game da shi ba ne, ƙauna na iya sa ka yin abubuwan hauka. "

A cikin wata sanarwa da aka buga a shafin Twitter bayan wasan Oscars din, Oscars din ya ce "ba ta yarda da zalunci ko tashin hankali ba ko ta wace hanya.

Rundunar ‘yan sanda Los Angeler LAPD ta tabbatar da cewa Rock ya ki gabatar da kara game da marin, tana mai cewa a cikin wata sanarwa, “Idan wanda abin ya shafa na bukatar kai kara nan gaba, LAPD za ta kasance a shirye don kammala rahoton tare da bincike.”

- Wannan labarin na jaridar The Hollywood Reporter ne wanda Hadiza Kyari ta fassara

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG