Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Fashin Teku Sun Kaiwa Wani Jirgi Farmaki a Najeriya


An kaiwa jirgin ruwan mai dauke da mutane 19 farmaki ne a yayinda yake dakon alkama daga Lagos zuwa Port Harcourt a Najeriya.

Barayin teku a Najeriya sun cafke wasu ma’aikata 12 na wani jirgin ruwan kasar Switzerland bayanda suka kai musu farmaki a daidai lokacinda jirgin ke harramar barin Nigeria.

Kafofin kamfanin safarar jirage na Massoel sun bada sanarwa jiya Lahadi cewa barayi sun abkawa jirgin ruwan nasu mai suna “MV Glarus” wanda ke da mutane 19 a cikinsa kuma yake dauke da kayan alkama daga Lagos zuwa Fatakwal.

Shima kamfanin dillacin labaran Reuters ya bayyana kasashen mutanen dake jirgin da abin ya shafa inda yace bakwai daga cikinsu duk ‘yan kasar Philippines ne yayinda sauran suka fito daga kasashen Slovenia, Ukraine, Romania, Croatia da kuma Bosnia.

Jami’an Najeriya sunce har yanzu ba’a san inda su wadancan ma’aikatan jirgin12 suke ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG