Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijirar Afurka Na Fuskantar Banbancin Launin Fata Yayin Da Amurka Ke Maraba Da 'Yan Ukraine


A cikin watan Maris, lokacin da Shugaba Joe Biden ya yi sanarwar maraba da 'yan gudun hijirar Ukraine 100,000, inda ya ba da matsayin kariya na wucin gadi ga wasu 30,000 da suke zama a Amurka tare da dakatar da hana korar 'yan kasar Ukraine.

Lamarin da ya sa tuni 'yan majalisar wakilai biyu na jam'iyyar Demokarat ba su bata lokaci ba wajen cewa ba a bai wa ‘yan kasar Haiti irin wannan damar jinkai din ba.

"Akwai duk wani dalili na nuna tausayi iri daya," abun da 'yar majalisar wakilai ta Amurka, Ayanna Pressley, daga Massachusetts, da Mondaire Jones, na New York, suka rubuta wa gwamnati kenan, suna masu cewa sama da 'yan Haiti 20,000 ne aka kora daga Amurka duk da ci gaba da rashin kwanciyar hankali a kasar ta Haiti biyo bayan kisan shugaban Haiti da girgizar kasa mai karfi a lokacin.

Haka zalika masu fafutukar kare hakkin bil adama na kasar Kamaru suka amince da kuma yin irin wannan kiran na neman agaji, inda suka gudanar da zanga-zanga a kofar gidan sakataren tsaron cikin gida na birnin Washington, Alejandro Mayorkas da kuma ofisoshin manyan mambobin majalisar a wannan watan.

Kiraye-kirayen nasu na zuwa ne a daidai lokacin da dubban daruruwan mutane a kasar Kamaru suka rasa matsugunansu a cikin 'yan shekarun nan sakamakon yakin basasar kasar da ya barke tsakanin gwamnatinta da ke magana da harshen Faransanci da masu amfani da harshen Ingilishi, da hare-haren kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram da sauran rigingimun yankin.

Wilfred Tebah bai damu da gaggautawar da Amurka ta yi na ba da kariya ga 'yan Ukraine da ke tserewa mummunar mamayar da Rasha ta yi wa kasarsu ba.

Sai dai matashin mai shekaru 27, wanda ya tsere daga Kamaru a lokacin rikicin da ake ci gaba da yi, ya na mamakin abin da zai faru idan miliyoyin da ke tserewa daga wannan kasa ta Gabashin Turai sun kasance wani launin fata ne na daban.

Yayin da Amurka ke shirin yin maraba da dubun-dubatar 'yan kasar Ukraine da ke tserewa yaki, kasar na ci gaba da korar dimbin 'yan gudun hijirar kasashen Afirka da Caribbean zuwa kasashen da ba su da kwanciyar hankali da tashe-tashen hankula inda suka fuskanci fyade, azabtarwa, kama su ba bisa ka'ida ba da sauran cin zarafi.

"Ba su damu da Bakar fata ba," in ji mazaunin Columbus, Ohio, da ya ke magana game da 'yan siyasar Amurka. “Bambancin a bayyane yake. Sun san abin da ke faruwa a can, amm sun yanke shawarar rufe idanuwa da kunnuwansu."

Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida, wacce ke kula da bada takarda ba da kariya ko kuma TPS da sauran shirye-shiryen jinkai, ta ki amsa korafe-korafen wariyar launin fata a manufofin shige da fice na Amurka. Har ila yau, ta ki bayyana ko tana yin la'akari da bayar da TPS ga 'yan Kamaru ko wasu 'yan Afurka, tana mai cewa a cikin wata rubutacciyar sanarwa kawai za ta "ci gaba da sa ido kan yanayi a kasashe daban-daban."

Hukumar ta fadi cewa, kwanan nan ta fitar da sunayen TPS ga Haiti, Somaliya, Sudan da Sudan ta Kudu -da dukkannin kasashen Afurka ko kasashen Caribbean - da kuma fiye da 'yan Afghanistan 75,000 da ke zaune a Amurka bayan da kungiyar Taliban ta mamaye ta kuma kwace kasar. . 'yan Haiti suna daga cikin mafiya yawa wajen cin gajiyar TPS, inda su ka kai fiye da 40,000 a halin yanzu.

Sai dai da alama, game da batun Ukraine, Biden ya nuna ya fi bada himma ne a fadadadden manufofin ketarensa a Turai, wato manufar da ta mai da hankali kan 'yan gudun hijira da baƙi, a maimakon nuna bambancin launin fata, in ji María Cristina García, farfesar tarihi a Jami'ar Cornell da ke Ithaca, New York.

Amma Tom Wong, wanda ya kafa cibiyar manufofin shige da fice ta Amurka a Jami'ar California, San Diego, ya ce a yanzu ne bambance-bambancen launin fata ya fi fitowa a fili.

"Amurka ta mayar da martani ba tare da bata lokaci ba ta hanyar ba da kariya ga fararen fata da 'yan gudun hijira wanda galibi ‘yan kasashenTurai ne," in ji shi. "Yayin da yawancin mutane masu launi daga Afurka, da Gabas ta Tsakiya, da Asiya suna ci gaba da kasancewa cikin wahala."

Bayan Kamaru, masu fafutukar kare bakin haure kuma suna jayayya cewa ya kamata Kongo da Habasha su cancanci samun agaji saboda rikice-rikicen da suke ciki da ya ki karewa, haka kuma da Mauritania, tunda har yanzu ana cigaba da bauta a can.

Kuma suna korafin cewa ana mayar da waɗanda suka fito daga wasu ƙasashe da nufin hana yaduwar COVID-19 a yayin da matakan ba su shafar masu neman mafaka da su ka fito daga Ukraine ba.

~ AP

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG