Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Gano Mota Shake Da Makamai A Las Vegas


Rahotanni daga Las Vegas sun bayyana cewa jami'an 'yan sanda na ci gaba da bincike domin gano dalilai dakuma bayanan sirri akan mummunan harin da ya yi sanadiyyar rayukan jama'a da dama a jihar Las Vegas dake nan Amurka.

'Yan sandan Las Vegas sun ce sun kama wata mota da suke nema a bincike da suke yi a kan mummunan harin bindiga da dan bindigar nan Stephen Paddock ya kai daga dakinsa dake cikin hawa na 32 na benen Otal din Mandalay Bay, inda ya kashe mutane 58 kuma ya raunata wasu daruruwa da suke halartan wani bikin kade kade da raye raye.

'Yan sandan sun fada a jiya Alhamis cewa sun gano motar kirar Hyundai Tucson, yayin da suke bincike a Reno a gidan da Paddock ke zaune da budurwarsa Marilou Danley.

Sai dai ba a gano ko 'yan sandan sun kama motar a jiya Alhamis ko dai cikin wannan mako ne kafin Alhamis din ba.

Tallafin da aka samu a gidauyar da aka kafa ta taimakawa iyalai da wadanda wannan harin bindiga na Las Vegas ya rutsa dasu da ya kai dala miliyan 9.5, kuma akwai alamar gidauniyar zata samu gomman miliyoyin dala, a cewar Kwamishinan lardin Clark Steve Sisolak bisa ga wani rahoton da aka buga a jaridar Las Vegas Sun.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG