Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baturen ‘Yan Sandan Las Vegas Ya Ce Zai Yi Wuya Maharin Ya Kitsa Harin Shi Kadai


Dangane da mummunan harin nan da wani mutum ya kai wanda yayi sanadiyyar hallaka mutane da dama a jihar Las Vegas ta kasar Amurka, shugaban Amurka Donald Trump ya kai ziyara a wurin da lamarin ya faru.

Yayin da akeci gaba a binciken musabbabin abinda ya haifar da harbin da ya hallaka mutane mafi muni a tarihin Amurka, Shugaba Trump ya kai ziyara a birnin na Las Vegas, a jiya laraba domin jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwan su da kuma wadanda wannan bala’in ya rutsa dasu, tare da wadanda abin ya faru gaban su.

A wuri daya Baturen ‘yan sandan na Las Vegas Joe Lambardo ya ce ya zama wajibi ayi Magana da duk wani wanda yasan wannan dan bindigar domin yiyuwar samun wani da suke da alaka ta fannin aikata irin wannan danyen aikin.

Ya kara da cewa ganin yadda Paddock, ya mallaki tarin makamai a ciki motar sa, Baturen ‘Yan sandan ya shaidawa manema labarai cewa zai yi wahala ace wai shi kadai ne ya kitsa wannan abu, ba tare da wani ba.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG