Accessibility links

​‘Yan Sandan Abuja Na Takurawa Masu Zanga-zanga


'Yan Sanda na takurawa masu zanga-zangar lumana a Abuja.

Masu zanga-zanga a cikinsu harda tsohuwar Ministan Ilimi, sun jaddada ‘yancinsu na gudanar da taron lumana, yayin da suke kira a dawo da dalibai su sama da 200 da ‘yan bindiga suka sace.

‘Yan Sanda Najeriya sun hana masu zanga-zanga shiga dandalin Unity Fountain dake Abuja Lahadinnan, inda ma sukayi ta ja-in-ja da mata da maza.

“A matsayina na ‘yar Kasarnnan, ina da ‘yancin gudanar da taron lumana, babu wanda ya isa ya hana ni wannan daman. Bazan je ko ina ba. Ina da ‘yancin zuwa ko ina a cikin al-ummarnan. Wannan demokradiyya ce, kuma ko lokacin mulkin soja nayi zanga-zanga, balle demokradiyya. Bazan je ko ina ba,” a cewar Oby Ezekwesili.

Hadiza Bala, daya daga cikin shuwagabanin masu gangamin cewa tayi “muna nan a wajen da muke zuwa kullum, domin tattaunawa, da gangamin lumana, kuma an hana mu, ance wai mu tafi, mu kuma mun ki, saboda baza mu bar kowa ya keta hakkin mu na bil adama ba. Na gode.”

“Baza mu je ko ina ba, kuma duk wanda yake son tafiya ya je, amma ni Oby Ezekwesili, bazan je ko ina ba. Babu inda zani,” a cewar Ms. Ezekwesili.
XS
SM
MD
LG