Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Yi Wuraren Kiwo 368 A Jihohi 25 Na Najeriya


Taron Kungiyar Makiyaya Ta Miyetti Allah A Najeriya
Taron Kungiyar Makiyaya Ta Miyetti Allah A Najeriya

A Najeriya, amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na samar da wuraren kiwo 368 a Jihohi 25, ya dauki hankalin manya manoman kasar, inda wasun su ke ganin an dauko hanyar magance yawan rikicin da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya.

Wasu jihohin sun fito fili karara sun ki amincewa da yunkurin. Amma masu ruwa da tsaki a fannin noma sun ce abu ne da ya kamata a yi tuntuni.

Wannan mataki da shugaba Buhari ya dauka ya biyo bayan shawarwari ne da wani kwamiti na musamman ya ba shi, wanda ya yi nuni da cewa samun wuraren kiwo zai taimaka wajen rage rikicin manoma da makiyaya da aka gagara samo bakin zaren tun da dadewa.

Shugaban kungiyar manoma ta kasa Arch. Kabir Ibrahim ya ce idan aka samu irin wanan gagarumin sauyi, ya kamata mutanen kasa su amince da shi saboda a gwada a gani.

Kabiru ya ce da jihohin Arewa da jihohin Kudu duk daya ake, ba abin da ya banbanta kasar sai ra'ayi, kuma bai kamata a bari ra'ayoyi su raba kan kasar ba. Ya kamata a hade wuri guda a yi wa kasa aiki da zai kawo ci gaba.

Shi kuwa mamba a majalisar gudanarwa ta hukumar tantance ingantaccen iri na kasa Ibrahim Musa ya ce wannan abu ne da ake da shi a kasa tuntuni, kuma in an mayar da shi yanzu yana da kyau.

Musa ya ce wadannan wuraren kiwon dama tun 1948 ake da su har zamanin su marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto an yi amfani da su a Jihohin kasar.

Musa ya kara da cewa yunkuri ne mai kyau wanda zai taimaka wajen tattara kan makiyaya a wuri guda, domin a tsugunad da su domin ba yadda za a a yi manomi ya rayu babu makiyayi yana mai cewa makiyayi ba zai rayu ba sai da manomi.

Ya kara da cewa yin hakan zai sa a samu abubuwan more rayuwa cikin sauki har a samu kudaden shiga sosai domin zai taimaka wa tattalin arzikin kasa.

Shi kuwa mataimakin shugaban kungiyar manoman auduga ta kasa Dokta Munzali Daiyyabu Taura ya ce lallai ya kamata manoma da makiyaya su sani cewa wannan yunkuri shi ne babban abin alheri ga al'umman kasa.

Dayyabu ya ce idan aka samu dama aka kirkiri wannan shiri na Rugga, zai kawo ci gaba sosai na samun tagomashi irin su makarantu, hanyoyin kiwon lafiya da ruwan sha musamman ga makiyaya.

Dayyabu ya ce wannan zai samar da sana'a a kasa kuma za a yi shi cikin halin fahimta, wanda zai kawo kwaciyar hankali.

Sai dai wasu jihohin Kudu maso Gabas, da Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma, har da wasu a Arewa irin su Jihar Binuwai sun fito fili sun ce su ba za su amince da samun wuraren kiwo a jihohinsu ba duk da cewa kwamitin ya ce sai an yi tuntuba tare da wayar da kan jama'a kafin a kai ga tabbatar da shi a jihohin.

Kwamitin ya yi aiki ne a karkashin shugaban ma'aikata na Fadar Aso Rock, Ibrahim Gambari, da gwamnonin Kebbi, Ebony da ministan albarkatun noma da ministan albarkatun ruwa da kuma ministan muhalli.

Saurari rahoto cikin sauti daga: Medina Dauda:

Za A Yi Wuraren Kiwo 368 A Jihohi 25 Na Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00


XS
SM
MD
LG