Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Kananan Hukumomi 44 A Kano Zai Lakume Sama Da Naira Miliyan Dubu 2


Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gudurinta na fitar da kudi Naira Miliyan dubu biyu da dari uku domin gudanar da zaben Kananan Hukumonin 44.

A cikin makon jiya ne, hukumar zaben jihar ta ce zata gudanar da zaben a ranar 16 ga watan Janairun shekara ta 2021.

Jadawalin zaben da hukumar ta fitar ya baiwa Jam’iyyun siyasa tsawon watanni uku su yi shirye shiryen da suka kamata domin tunkarar zaben.

A zantawa da Muryar Amurka, Shugaban hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka yace baya ga tsare tsare da ganawa da daukacin masu ruwa da tsaki domin samun nasara, hukumar ta fitar da farashin takardun shiga zabe ga ‘yan takara.

A wannan karon dai hukumar zaben ta Kano tace kamfanonin cikin gida zata baiwa kwangilar buga takardun zabe domin rage kudaden da take kashewa. To amma, Comrade Sa’idu Bello jigo a Jam’iyyar hamayya ta PDP na cewa babu dalilin tauwala kudin Fom saboda idan a wane aka buga da dalar Amurka hukumar zata biya.

Yayin da Jam’iyyar PDP ke kokawa kan kudin takardun shiga zabe, ita kuwa Jam’iyyar APC dake Mulki na cewa hakan ya yi dai-dai a cewar Hon Ibrahim Zakari Sarina sakataren Jam’iyyar a jihar Kano.

Tuni dai shugaban hukumar zaben ta Kano ya ce zai tabbatar da adalci ga dukkanin Jam’iyyu da zasu shiga zaben. Sai dai Jam’iyyun hamayya na bayyana shakku.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti:

ZABEN KANANAN HUKUMOMI A KANO 2020
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00


Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG