Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Da Trump Ya Kai A Kenosha Ta Haifar Da Cece Kuce


Trump a birnin Kenosha
Trump a birnin Kenosha

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ziyarci wasu yankunan birnin Kenosha na jihar Wisconsin a jiya Talata, da aka lalata a tashin hankalin da ya faru makon da ya gabata.

Tashin hankalin ya faru ne bayan da farar fata dan sanda ya harbi bakar fata mai suna Jacob Blake har sau bakwai a bayansa, yayin da jami’in dan sandan ke kokarin kama shi.

“Dole ka yanke hukunci, dole ka zama mai karfin hali, dole ka zamanto mai karfi, kuma dole ka yi shirin kawo mutane domin dakatar da tashin hankali," a cewar shugaban na Amurka lokacin da yake musayar yawu da jami’an tsaro.

Trump da abokin hamayyarshi na jam’iyar Democrat Joe Biden suna bayyana ra’ayoyi mabanbanta a kan wanda zai iya tabbatar da zaman lafiya a kasar yayinda ya rage watanni biyu a gudanar da zaben shugaban kasa. Trump yana caccakar ‘yan jam’iyar Democrat da sakaci, yana mai cewa, “tilas ne mu kara ba jami’an tsaronmu goyon baya.”

Trump ya ce “Masu zanga-zangar tayar da hankali sun ruguza ko lalata akalla wuraren kasuwanci 25 na garin Kenosha, sun kone gine-ginen jama’a, tare da jifan jami’an ‘yan sanda da duwatsu, lamarin da ‘yan sandan ba zasu lamunta ba.”

To sai dai Trump bai gana da iyalan Blake a ziyarar da ya kai ba, amma ya yi ta nanata cewa ya yi magana da faston iyalan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG