Nasarar Trump a Indiana ta sa Cruz janyewa daga takarar shugaban kasa a jam'iyyar Republican

Donald Trump ke nan yana godewa magoya bayansa jiya bayan ya kada abokin hamayyarsa Ted Cruz

Senata Ted Cruz, mai wakiltar jihar Texas a majalisar dattawan Amurka ya janye daga takarar shugabancin Amurka, bayanda attajirin nan Donald Trump yayi masa mummunar kaye a zaben fidda gwani da aka yi a jihar Indiana, jiya Talata.

Cruz, ya gayawa magoya bayansa a birnin Indianapolis cewa, "babu damar ya ci gaba, domin masu zabe sun gwammace wani."

Trump ya sami gagarumar nasara a zaben na jihar Indiana, senata Cruz yazo na biyu, sannan gwamnan jihar Ohio John Kasich yazo na uku.

Trump ya "yaba da irin nasarar da ya samu a jihar Indiana," daga nan ya yabawa Cruz,da kuma sauran 'yan takara su 15 wadanda ya kira gwarzaye masu basira. Daga nan yayi kira da a hada kai a jam'iyyar ta Republican.

Shugaban jam'iyyar Republican Reince Priebus, ya kira Trump a zaman "dan takarar jam'iyyar mai jiran gado".

Amma wani kakakkin gwamnan jihar Ohio wanda yake takara har yanzu yana cewa, gwamnan har yanzu yana ganin za'a fafata a dandalin babban taron jam'iyyar a watan Yuli, inda yake ganin zai sami nasara idan zabe yaje zagaye na biyu.

A bangare 'yan Democrats kuma, an ayyana senata Bernie Sanders, ya doke madam Hillary Clinton a zaben na Indiana.

Duk da nasarar da Sanders ya samu a jihar Indiana, Clinton tana gaba dashi nesa ba kusa ba a yawan wakilai, kuma kusan za'a iya cewa da wuya ace ya cimmata.

Ted Cruz wanda ya sha kaye a Indiana ya kuma janye daga takarar