Dubban masu zanga-zanga sun yi tattaki a birnin Paris don neman a soke dokar da ta yarda da auren jinsi daya, watanni 6 kafin zaben shugaban kasa a Faransa.
‘Yan mata 21 cikin sama da 200 da aka sace sun sake haduwa da ‘yan uwansu, bayan rike su na tsawon kusan sama da shekaru biyu da kungiyar Boko Haram ta yi.
Labarin wasu 'yan bindiga sunkai hari a garin abalak dake cikin jihar Tahoua a kasar Nijer a daren juma a kan gidan mai garin abalak malam Hamed Bilu Moh’d Muktar.
Hira da Ministan Harakokin Cikin Na Nijar Malam Bazoum Mohamed
Masu zanga zanga sun yi gangami don nuna rashin amincewarsu kan wata yarjejeniyar cinikayyar iskar Gas kan dala milhan dubu 10 da kasar ta kulla da Isra’ila, suna cewa yarjejeniyar ba zata amfani al’umar kasar ba.
Wata kungiya mai fafutukar ganin an sako ‘yan matan Chibok sama da 200 da Boko Haram take garkuwa da su, tana barka da aka sako wasu 21.
Kungiyar Boko haram ta sako ‘yan mata 21 daga cikin 276 da su ka sace su tun watan Afrilun shekarar 2014.
Wasu mata sun zargi dan takarar shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican da neman yin lalata dasu.
Gwamnati ta ce tana yin sauyi ga tsarin zaben kasar wanda ya danne ‘yan adawa, ya kuma haddasa mummunar zanga-zangar wata da watanni.
Dubban musulmi ‘yan Shi’a sanye da bakaken kaya sun yi tururuwa zuwa Karbala da ke Iraqi domin fara bikin Ashura.
Bayan wata Mahaukaciyar guguwa Hurricane Mathew da ta doshi Florida sai kuma wata Mumunar Ambaliyar Ruwa A Carolina, Oktoba 12, 2016
Cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Amurka (USIP) ta yi taro da manema labarai talatan nan babban birnin Washington DC. Oktoba 11, 216
Kamfanin Samsung ya dakatar da kera tare da sayar da wayar Galaxy 7, bayan da rahotanni suka nuna cewa tana kamawa da wuta.
Alkalai za su yi wani zaman gaggawa bayan da hukumar tsaro ta farin kaya, wato SSS ta tsare wasu alkalai bakawai bisa zargin karbar cin hanci.
NIGER: Bikin Bude Taron Majalisar Dokokin Kasar Nijar
Kenya: Kampanonin kayan shafe-shafe a Kenya suna cin moriyar harajin da gwamnatin kasar ke dorawa akan kayan shafe-shafe daga kasashen waje yayin da sha’awar kayan mai rahusa, mara kemikal, kuma na cikin gida ke ta karuwa.
Norway: Shugaban kasar Columbia Juan Manuel Santos ya lashe lambar yabo ta Nobel ta zaman lahiya, a kokarinsa na kawo karshen yakin basasa a kasar sa.
Birni mafi girma a Najeriya, watau Legas ya zama guri mai muhimmanci wajen yada wani sabon wasan hawa igiyar ruwa - wato surfing.
Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya hadu da shugabanin Vietnam, inda ya yi musu alkawarin bunkasa huldar kasuwanci har ta Dala Biliyan biyu a nan gaba.
Domin Kari