Sojojin da aka tura domin dawo da doka a watan Yuni sun kashe mayaka bakwai ciki har da wasu shugabanni ‘yan aware uku.
Hukumomin tashoshin teku na wasu kasashen Afirka ta yamma sun daura damarar yaki da barayin teku da ke barazana ga lamuran kasuwancin teku a yankin.
Hauhawar hare-haren 'yan-bindiga da kuma sace mutane domin neman kudin fansa a Lardin Zazzau ya sa al'umma da malamai da kuma shugabannin yankin shirya taron addu'oin neman mafita game da wadannan irin matsaloli.
Amurka ta ayyana wasu shugabannin mayakan Houthi guda biyu wadanda ke da alaka da ayyukan da ke ci gaba da haifar da rikici a Yemen, wanda ke zama babbar barazana ga fararen hula, da kuma kara munin bala’in jinkai a can.
Da marecen jiya ne gwamnan na Kano ya yi wata ganawa da manema labaru a Kano kuma ya amsa wasu tambayoyi daga garesu.
A Najeriya, a wani abu mai kaman mayar da martani ga masu kiran majalisar dokokin kasar 'yar amshin shata, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce, ko kadan Majalisar ba 'yar amshin shata ba ce domin kuwa takan yi musayar yawu da bangaren zartaswa.
Majalisar dokokin Hong Kong ta zartar da sabuwar doka wacce ta yi wa tsarin zaben Hong Kong garambawul, wanda ya ba wa Beijing babban iko kan Hong Kong.
Yau talata 15 ga watan Yuni ake fara zagaye na 2 na kamfen riga kafin cutar covid 19 a jamhuriyar Nijer inda za a kafa asibitocin tafi da gidanka a mashigar ma’aikatun gwamnati tashoshin shiga motocin haya da filayen jirgin sama da gidajen hakimai da masu unguwa .
A Najeriya nau'in mutanen da ake kira zabiya ko Albino a turance sun ce cutar covid 19 ta haifar musu da babbar illa wadda har ke barazana ga salwantar rayukan su.
Maniyyata aikin hajin bana da masu kamfanonin jigilar alhazai ta jirgin yawo a Najeriya na bayyana alhini dangane da sanarwar hukumomin Saudiyya na janye aikin hajji ga ‘yan kasashen waje.
Ilimantar da ‘yan mata na daya daga cikin abubbuwa masu muhimmaci domin fitar da mutane daga talauci, rage rashin daidaito, kuma zai iya aza tubalin ci gaban tattalin arziki.
Ma'abota lamuran zabe da siyasa na cewa dawo da hakkin gudanar da zaben fidda gwani hannun hukumar zabe ne zai gyara harkar dimokradiyya a Najeriya.
A karon farko Majalisar Dattawan Najeriya ta ce ba ta riga ta dauki mataki akan takaddamar da ke gudana tsakanin Mahukuntan Najeriya da Kamfanin sadarwa na twitter ba.
A shekarar 2015, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Anabi a matsayin Rikakken Dan Ta’addan Duniya, inda ta rufe duk dukiyarsa da bukatunsa a cikin dukiyar da ke karkashin ikon Amurka
Yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke umartar gwamnonin kasar su hada hannu da masu rike da sarautu da shugabannin kananan hukumomi domin tabbatar da tsaro a yankunansu, karamar hukumar Ungogo a jihar Kano ta kaddamar da cibiyar yi wa Jama’ar yankin rijista.
Amurka ta yi Allah wadai da matakin hana amfani da Twitter da hukumomin Najeriya suka dauka tana mai cewa hakan "ba shi da gurbi a tsarin dimokradiyya.
A Najeriya, Sanatocin Jihohin Arewa sun koka kan sha'anin tabarbarewar tsaro a yankin. Wanan ya biyo bayan wani taron gaggawa ne da suka yi a Majalisar. To sai dai masu ruwa da tsaki na cewa kukan Sanatocin ihu ne bayan hari.
Bayan lafawar hare-haren 'yan-bindiga a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, yanzu 'yan-bindigar sun fara tare hanyar Kaduna zuwa Zariya inda a makon nan su ka kashe wasu matafiya sannan suka sace wasu.
Domin Kari