Yayin da ake yawan zargin matasan Fulani da garkuwa da mutane don neman kudin fansa, shugabannin Fulani sun yi tir da duk matasan da ke aikata hakan. Amma sun ce yayin da su ke Allah wadai da wannan rashin fulakun, su na so a binciki musabbabin aukuwar hakan saboda a magance shi dindindin.
Yayin da 'yan Najeriya ke cigaba da dandana kudarsu a hannun nau'ukan miyagu a fadin kasar, a daya gefen kuma, su na dada matsa lamba ma gwamnatin kasar da ta motsa miyagun su san da hukuma.
Wasu mazauna kauyen Buthidaung sun ce wani jirgin sama mai saukar ungulu na soji ne ya kai hari kan wani gungun ‘yan Rohingya, wadanda ke tara itacen gora a ranar Alhamis.
Firaministan Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, Fayez Sarraj, ya kira matakin na Janar Haftar yunkurin juyin mulki.
Shugaba Trump ne ya nada Alles, kuma ya kasance a kan wannan matsayin na tsawon shekaru biyu. Babu wani bayani ga jama’a kan dalilin sallamar shi.
Yayin da bangarori ke ta barin wuta kan juna a kasar Libiya ta yadda farar hula ke fama, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangaren Janar Khalifa Haftar bangaren gwamnati da su kwance damara.
Matsalar tsaron Zamfara ta dau wani sabon salo bayan da rundunar 'yan sandan Najeriya ta soke takardar izinin hakar ma'adanai a jahar ta kowa da kowa tare kuma da gaya ma 'yan kasashen waje da ke hakar ma'adanai a jahar su san inda dare ya masu.
Yayin da masu sace mutane ke cigaba da cin karensu ba babbaka musamman ma a arewacin Najeriya, wani dan jarida da aka taba sacewa ya kuma ga irin tashin hankalin da wadanda aka sace kan gani, ya ce a gaskiya a tashi a yi abin yi.
Sabanin yadda a baya 'yan arewacin Najeriya ke jin labarin sace mutane a kudancin kasar, yanzu ba ma sace mutane ake yi kawai a arewar ba, na arewar ma nema ya ke ya fi na kudu yawa da tsanani.
'Yan sandan kasar Uganda sun shiga farautar wasu 'yan bindigan da su ka sace wata ba-Amurkiya 'yar yawon bude ido tare da direbanta
A 'yan kwanakin nan, kamfanin na Facebook na fuskantar suka kan yadda ake amfanin da shafinsa wajen yada labaran bogi ko kuma wani abu da jama'a bai kamata su gani ba.
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan shafe tsawon mako guda da aka yi ana ta zanga-zangar nuna bijirewa ga shugaban kasar da gwamnatinsa.
A baya, Shugaba Donald Trump ya iyakanta adadin ‘yan gudun hijirar da kasar za ta iya tsugunarwa zuwa 30,000.
A cigaba da murza gashin bakin da ake yi tsakanin Amurka da kasar Mekziko saboda zargin barin bakin haure da ratsawa da kasar zuwa cikin Amurka, Shugaba Donald Trump ya ce Mekziko ta hana bakin hauren ko kuma a sake lale.
A wani cigaba da sojojin da ke fafatawa da 'yan Boko Haram su ka samu, sojojin sun hallaka wani gagararren kwamandan Boko Haram mai ido daya da shi da zafafan mayakansa.
A wani al'amari mai bakanta rai, mutanen jahar Bauchi sun yi rashin wasu bayin Allah wajen 13 a wani hadarin mota, baya ga wasu kuma da su ka ji raunuka.
Garkame al'ummar musulmi musamman 'yan kabilar Uighur da sauran tsirarun al'ummomin musulmai da China ta ke yi a wasu sansanoni, ya ja hankalin Amurka, wadda ta yi tir da hakan, tare da kiran China ta daina.
Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin bincike na musamman na Robert Mueller ya mika sakamakon rahotonsa, inda ya ce ba a ga shaidar cewa kwamitin yakin neman zaben Trump na shekarar 2016 ya hada baki da Rasha ba.
Yayin da, a daya gefen, Shugaban Amurka Donald Trump ya yabi kwamitin binciken da ya ce ya wanke shi, a daya gefen kuma, ya caccaki 'yan jam'iyyar Dimokarat, wadanda ya ce su na masu bita da kullin siyasa.
Yayin da adadin wadanda su ka rasa rayukansu a bala'in mahaukaciyar guguwar Idai ke karuwa, Majalisar Dinkin Duniya ta shiga neman taimako a madadin wannan kasa ta kudancin Afirka.
Domin Kari