Rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar APC shiyyar Zamfara ya dau wani sabon launi, bayan da kotun daukaka kara ta ce babu shaidar cewa jam'iyyar ta APC ta gudanar da zaben fidda gwani a Zamfara, duk kuwa da lashe zabukan da ta yi a jahar.
Bayan kikikaka da ja-in-jar da aka yi ta yi - har da zuwa kotu, a karshe hukumar zaben Najeriya ta ayyana tsohon Ministan Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed Duguri (Kauran Bauchi) na jam'iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jahar Bauchi.
Abin kamar almara; yanzu kungiyar ISIS, wadda a baya ta girgiza duniya, har ta kafa babbar daularta, wadda ta kunshi akasarin kasar Iraki da sassan Siriya, ta zama tarihi, a kalla ta fuskar daula da dakaru.
Yanzu haka an yanke wa babban limamin Cocin Katolika na Faransa hukuncin daurin watannin shida, saboda kin sanar da hukumomi laifin lalata da wani Firist ya aikata.
Bayan wasu shekaru da dama, yanzu haka kasar Brazil da Amurka sun bude wani sabon shafi na hulda tsakanin kasashen biyu mafiya girma a yammacin duniya.
An tabbatar da aukuwar wani bala'i a Afurka, bayan da Shugaban kasar Mozambik, ya tabbatar cewa sama da mutum dubu sun mutu a kasar, bayan da wata mummunar guguwa dauke da ruwan sama ta ratsa ta kasar, a makon da ya gabata.
A cigaba da bayar da mamaki da 'yan Najeriya ke yi a fannoni daban-daban na rayuwa a fadin duniya, wani yaro dan asalin Najeriya mai shekaru 8 ya zama zakara a gasar da aka yi a birnin New York na nan Amurka
An bude wani sabon babi a takaddamar sakamakon zaben Shugaban Kasa a Najeriya, bayan da jam'iyyar PDP ta shigar da kara a kotun daukaka kara don kalubalantar ayyana Shugaba Buhari na jam'iyyar APC da aka yi a matsayin wanda ya ci zaben.
Jayayya kan makomar zaben gwamnan jahar Bauci sai abin da ya yi gaba, duk kuwa da shirin bayyana sakamakon zaben a yau dinnan, bayan da hukumar zabe ta INEC ta sauya shawara ta wajen tsame jahar Bauci daga jerin jahohin da ta ayyana zabukansu marasa kammala.
A wani al'amari mai kama da yinkurin kawo karshen yakin Sudan Ta Kudu, 'yan tawayen Sudan ta Kudu na kira ga masu ruwa da tsaki da su matsa ma Shugaba Salva Kiir ya saki kudi a yi aikin sasantawa.
Mai tsattsauran ra'ayin fifita farar fata kan sauran jinsunan nan da ya kai mummunan hari a kasar New Zealand ya fara gurfana a gaban kotu, inda wasu dogarawan tsaron kotu dauke da manyan bindigogi su ka shigo da shi.
An gurfanar da wasu shahararrun mutane 50 a gaban kotu, saboda wata badakala mafi girma ta bada kudi domin shiga wasu manyan makarantu a Amurka.
Yanzu haka kasashen duniya da dama sun bada umarnin hana amfani da irin wannan jirgi na Boeing 737-Max 8. tun bayan da irinsa ya fadi a kasar Habasha a satin da ya gabata.
Yayin da 'yan jam'iyyar APC ke cigaba da shagulgulan nasarar zabe a jahar Borno, wasu 'yan PDP na ganin da kamar wuya a ce dinbin wadanda su ka yi rajista sun fito sun kada kuri'a kamar sam babu wanda ya mutu ko kuma ya kaura.
A cigaba da cece-kucen da ake yi kan batun ayyana zabe a matsayin mara kammala saboda wasu dalilai, gwamnan jahar Sakkwato kuma dan takarar gwamnan jahar karkashin jam'iyyar PDP, wanda kuma lauya ne, ya ce a bincikensu ba su ga wannan tanaji a wata doka ba, don haka za su ruga kotu.
Idan aski ya zo gaban goshi, aka ce, ya fi zafi. Yanzu haka 'yan takarar gwamnan jahar Kano a karkashin jam'iyyun APC da PDP na nan sun zaku su ji sakamakon zaben gwamnan jahar Kano, daya daga cikin jahohi biyu mafiya yawa a Najeriya. Hasali ma, 'yan Najeriya da dama na dokin jin wannan sakamakon.
Bayan wani hari da aka kai a yankin Kashmir da ke karkashin ikon India, wanda ya hallaka mutane da dama, yanzu haka Pakistan ta ba da sanarwar damke shugaban kungiyar da ake zargi da kai harin.
Trump ya shiga nuna matukar bacin ransa game da takardun neman bayanai da kwamitin shari'a na majalisar wakilai karkashin Jerrold Nadler su ka aika ga wasu makusantansa da zummar bincikensa.
Duk da sassautowar da Shugaban Aljeriya ya yi kan sha'awar shugabanci na mutu-ka-raba, 'masu zanga-zangar bukatar ya je ya hutu ba su gamsu da alkawarin da ya yi na rage tsawon wa'adinsa ba.
Ga dukkan alamu an shiga wani babi a dambarwar siyasar Amurka, ganin yadda 'yan jam'iyyar adawa ta Dimokarat, masu rinjaye a Majalisar Wakilai, su ka kaddamar da jerin bincike kan Shugaba Donald Trump.
Domin Kari