Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kai ziyara jihar Benue domin jajintawa da kuma kiran jama’a su a zauna lafiya, saboda rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da jihar ke fama da su.
Zamantakewar Jama'a
Yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan dokar sa haraji kan karafa da dalmar kasashen waje, Tarayyar Turai ta ce ba ta san makomarta kan wannan batu ba.
Ta leko ta koma ga mabukata a yankin Ghouta da yaki ya daidaita a kasar Siriya, bayan da tawagar motocin dakon kayan agaji su ka isa da dinbin kayan tallafi amma su ka kasa saukewa saboda yanin tabarbarewa tsaro.
A wani al'amari na bazata, Shugaban Amurka Donald Trump ya amince ya gana da mutumin da su ka yi ta musayar zafafan kalamai da shi, wato Shugab Koriya Ta Arewa. Amma wasu na yabawa wasu kuma na shakka.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jahar Filato a cigaba da kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar da kuma kaddamar da ayyukan cigaba.
Yayin da gwamnan jahar Ikko ke kokarin yada harshen Yarbanci ta wajen amfani da kananan makarantu, wasu da ba Yarbawa ba na nuna damuwa da bargabar yiwuwar hakan ya janyo kabilanci.
Yayin da mata a fadin duniya, musamman ma a wurare irin arewa maso gabashin Najeriya ke takaicin irin cin zarafi da danniyar da ake nuna masu, yau a fadin duniya ana harkokin jaddada zagayowar ranar mata ta duniya.
Ganin yadda al'ummar Musulmi tsiraru na kasar Sri Lanka ke shan azaba a hannun 'yan kabilar Sanhalese mabiya addinin Budda, gwamnatin kasar ta katse hanyoyin sada zumunta, wadanda ta nan ne ake shirya tashe-tashen hankulan.
Yau ana zaben Shugaban kasa a Saliyo, kasar da tattalin arzikinta ya durkushe saboda fama da annobar Ebola da ta yi a shekarar 2014.
Ga dukkan alamu za a shiga gasa a kasuwannin duniya tsakanin manyan kasashe saboda martanin da kasar China ta ce za ta mayar muddun Amurka ta sa haraji kan karafa da dalmar kasashen waje.
A wani mataki na inganta huldar diflomasiyya da tattalin arziki da tsaro tsakanin Amurka da Afirka, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, zai kai ziyara Afirka daga ranar 6 zuwa 13 ga wannan wata na Maris.
Yayin da ake fargabar yiwuwar fuskantar gasa a kasuwannin duniya sanadiyyar sa haraji da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yi kan karafan kasashen waje, Trump ya kare matsayinsa
Zargin almundahanar da ake ma Firaministan Isira'ila Benjamin Netanyahu ya dau wani sabon salo, bayan da 'yan sanda su ka je gidan Netanyahu don gudanar da bincike.
An kai hare-hare kan Ofishin Jakadanci da kuma cibiyar raya al’adu ta kasar Faransa da ke Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso.
A cigaba da takaddamar da ake yi tsakanin Shugaba Donald Trump na Amurka da Shugaban Mekziko Enrique Pena Nieto, saboda shirin Amurka na gina katanga tsakaninsu, Shugaban na Mekziko ya ce ya ma fasa zuwa Amurka.
A wani al'amari mai kama da shirin shugabanci na mutu-ka-raba, jam'iyyar kwamines mai mulkin kasar na shirin cire wa'adi a kundin tsarin mulkin kasar.
Rigimar yankin ruwan Koriya ta dau wani sabon salo da ka iya sa kura ta lafa, bayan da Koriya Ta Kudu Ta ce Koriya Ta Arewa za ta so ganawa da Amurka.
Domin Kari