A martaninsa ga samamen da jami'an Hukumar Yaki Da Almundahana ta EFCC ta kai gidansa, tsohon gwamnan jahar Sakkwato, ya ce abotansa da Sambo Dasuki ya zarce batun kwangila, wadda bai ma taba karba daga gareshi ba.
Yayin da jama'a ke sauraron sakamakon zaben da aka gudanar a jahar Kogi ta yankin tsakiyar Najeriya, masu ruwa da tsaki na yabawa da yadda aka gudanar da zaben
A wata hobbasa ta bunkasa noman rani a Najeriya, gwamnatin kasar ta zabi jahar Kebbi don kaddamar da noman rani na wannan shekarar, ganin yadda jahar ta fi kowacce noma shinkafa da alkama, wadanda aka fai ci a Najeriya
Alhaji Suleiman Ibrahim Sambo ya sami amincewar gwamnatin jahar Taraba a matsayin Saki (Kpanti) Zing.
Da alamar dai muddun hukumomin da abin ya shafa ba su tashi haikan ba, to karancin mai zai cigaba da galabaitar da arewacin Najeriya.
Majalisar Dinkin Duniya ta kuduri aniyar yakar talauci a karkara a janhuriyar Nijar ta wajen tayar da komadar mazauna karkara.
Kamar yadda aka zata, duk da abin da wasu ke zargin tursasawa ce ta gwamnati, jam'iyyar adawa ta gwamnati ta tsai da Kassim Mukhtar a matsayin dan takararta
Yayin da ake ta korafe-korafen cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta tafi da mata yadda ya kamata ba, wata fitacciyar 'yar rajin muradun mata ta ce lokaci bai yi na zargin gwamnatin Buhari da kin tafiya da mata ba.
Idan rahotannin da ke fitowa daga Janhuriyar Nijar su ka tabbata to shakka babu kasar ta fara shiga wani sabon babi na rigimar siyasa.
A kokarinsa na kara karfin gwiwa ma 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce da yaddar Allah kashin 'yan Boko Haram zai bushe kwanan nan.
Da alamar dai siyasar Janhuriyar Nijar za ta kara armashi kwanan nan ganin Kassim Moktar ya bayyana aniyarsa ta shiga yakin neman zaben gadan-gadan
Yayin da sabbin ministocin Najeriya ke harmar fara aiki, matasan kasar na cigaba da korafin rashin tafiya da su a gwamnatin Buhari
Da alamar gwamnatin Najeriya za ta fara aiwatar da abubuwan da ta yi alkawarinsu ga 'yan kasar gadan-gadan daga yanzu ganin sabbin ministocinta sun tare a ofisoshinsu a Abuja, babban birnin kasar
Bangarorin APC da PDP na cigaba da cece-kuce kan hukuncin kuton daukaka kara, wadda ta soke zaben Gwamna Darius Ishaku a matsayin gwamnan jahar Taraba.
Yayin da Najeriya ke kara azama a yaki da cin hanci da rashawa, wani kazamin rikici ya barke tsakanin sojoji da direban motoci kan abin da aka ce na da nasaba da karbar na goro
Sojojin Najeriya sun yi ikirarin sake samun wata nasarar, inda har su ka kubutar da waasu mutane 20 akasari yara da mata
Sayar da man fetur sama da farashin gwamnati ya janyo rufe wasu gidajen mai a jahar Osun.
An yi abin tarihi a Najeriya. An samu zababbiyar gwamnar jaha mace ta farko.
Yayin da ake ta cece-kuce kan makomar wasu ministoci, Shugaba Buhari ya bayyana cewa babu Ministan da zai yi zaman kashe wando.
Ana taro kan jaddada muhimmancin aiwatarwa da kuma mutunta shawarwarin da aka cimma a taron kasashe rainon Faransa
Domin Kari