'Yan Najeriya na cigaba da kara mai da hankali kan bayyana abubuwan da su ka fi haddasa almundahana a kasar; su na masu kiran da a kyamaci sanadojin almundahanan.
Ribibin kwamitoci masu romo da 'yan Majalisar Tarayyar Najeriya ke yi na cigaba da sa 'yan Najeriya cece-ku ce kan makomar kasar ganin wasu 'yan majalisar kasar sun fi kokarin ciyar da kansu da iyalinsu gaba.
Dubun wasu mayaudara da sunan 'yan gudun hijirar Boko Haram ya cika, bayan da su ka bayyana kansu ta wajen rashin gaskiya.
Jam'iyyun Adawa a Janhuriyar Nijar na zargin an bai wa shugabannin al'umma (barumai) cin hanci don shirin magudin zabe
Yayin da siyasar Janhuriyar Nijar ke cigaba da zafi, 'yan adawa sun yi gangamin nuna rashin amincewarsu da abin da su ka kira shirin yin magudi
Yayin da ake kokarin gano dalilin faduwar jirgin saman Rasha a kasar Masar, 'yan Rasha na makokin tunawa da mutanenta a yau Lahadi
Hankalu sun tashi a birnin kasar Somaliya, bayan da kungiyar al-Shabab ta kai wani mummunan harin da ya sa wani otel yin jina-jina.
A wani cigaba a kokarin da ake na samun mai a arewacin Najeriya, jahar Bauci da wani kamfanin hako ma'adinai na kasar Rasha na shirin hako mai a Baucin.
Jama'ar jahar Naija na makokin rashin daya daga cikin iyayen kasa, Mai Martaba Sarkin Borgu, Alhaji Halliru Dantoro
Kasar Rasha ta ga wani mummunan bala'i bayan da jirgin wani kamfanin kasar ya rikito da mutane 224 kuma ana jin babu wanda ya rayu.
Yayin da gwamnatin Najeriya ke cigaba da nade-naden jami'anta, matasa na kokawa kan rashin sasu cikin gwamnati
Jam'iyyar PDP ta sha kaye a shari'ar da aka yanke kan zabe a jahar Filato, wadda ta tabbatar da nasara ga jam'iyyar APC.
Yayin da ake ta kiraye-kirayen a taimaka ma jami'an tsaron Najeriya a yaki da Boko Haram, rundunar sojin Najeriya ta ce dakura 'yan Boko Haram da aka yi ya sa su ke ta kokarin nuna cewa har yanzu su na da karfi, ta wajen kai hare-hare.
Yayin da zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya ke cigaba da ganin sauye-sauye, ciki har da tsarin rajistar samun lambar shaidar mallakar ajiya a banki, kwararru na cigaba da bayyana muhimmancin wadannan matakan
Da alamar dai haka ta fara cim ma ruwa, game da shiga sojojin Amurka kasar Kamaru don taimakawa wajen yakar Boko Haram saboda a yanzu ta tabbata cewa an fatattaki 'yan Boko Haram daga garin Kerawa na Kamaru.
Mutanen Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun tashi haikan wajen yin fito-na-fito da yinkurin canja kundin tsarin mulkin kasar, wata al'ada ta 'yan siyasar Afirka masu neman yin tazarce
Yayin da hukumar EFCC ke zafafa kamenta, masu fashin baki a Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu.
Kasar Kamaru, wacce ke makwabtaka da Najeriya inda Boko Haram ke da asali, wadda don haka ita ma ke fama da Boko Haram din, ta samu gudunmowa daga kungiyar Tarayyar Turai.
Yayin da ake harmar rajistar Fulani a yankin kudu maso yammacin Najeriya, ana samun banbancin ra'ayi game da rajistar.
Yayin da jama'a ke ta korafe-korafe game da batun sabbin Ministocin da za a nada a Najeriya, an yi bayanin sauyin da aka yi wajen tantance wadanda za a nada din da kuma kokarin da ake yi na ganin an tantance tsohon gwamnan jahar Rivers cikin natsuwa.
Domin Kari