An sami munanan hadarorin jiragen sama a Scotland da Mozambique da su ka yi sanadin mutawar mutane da dama
A cigaba da nuna rashin yaddar ta da sakamakon zaben gwamnan jihar Anambara, jam'iyyar APC shiyyar jihar Oyo ta yi zanga-zanga
An bayyana yadda harkar ilimi ta durkushe a Nijeriya da cewa wani abin bakin ciki ne da kunya ga kasa irin Nijeriya.
Magabatan arewacin Nijeriya sun sake nuna damuwarsu game da halin da yankin ke ciki ta fuskar tsaro da tattalin arziki.
An sami asarar rayuka da na dinbin dukiyoyi sanadiyyar aukuwar wani tashin hankali a garin Kuka da ke Karamar Hukumar Shendam ta jihar Filato.
Manyan kasashen duniya shida da kasar Iran sun cimma ma wata yarjajjeniya, wadda ta kawo karshen shirin nukiliyar Iran da ake takaddama akai,
Gwamnatin jihar Filato ta dage zabukan fidda da dan takara na kananan hukumomin Wase da Jos Ta Arewa.
Matan Shugabannin kasashen Afirka sun shirya wani taron wuni guda a Nyamai babban birnin Janhuriyar Nijar kan yaki da sayar da muggan kwayoyi bisa titi da al’amarin ya yi yawa a akasarin kasashen Afirka.
Yau a birnin Lagos na Nijeriya, Ma’aikatar Kudin Nijeriya ta kaddamar da tsarin inshorar nan na Takaful.
Hamshakin dankasuwa kuma shaharraren dan siyasar nan na Sakkwato da wasu miyagu su ka sace shi kwanan baya mai suna Alhaji Abu Dankure ya rasu da asubahin yau.
Wata kwararrar mai ilimin zamantakewa da halayyan dan adam (sociologist) ta ce irin tarbiyyar da al'umma ta ba da matasanta za ta shata rayuwarsu da ta al'ummar kasar nan gaba.
Gwamna Murtala Nyako na jihar Adamawa ya ce jam'iyyar PDP mai mulki ta fara masu bita-da-kulli ta wajen cinna masu hukumar EFCC da sauran makirce-makirce.
Wani sabon tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a birnin Trabulus na Libiya, ya janyo rufe makarantu da wararen sana'a a wasu unguwanni.
Ana nan ana ta shirin gudanar da zaben Gwamnan jihar Anambara a gobe Asabar.
Karin wa'adin dokar ta baci a jihar Borno ya janyo korafe-korafe daga wadanda hana buga wayar da dokar ke yi ke shafar sana'o'in su.
Gwamna Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe na zargin mutumin da ya gada da rub da ciki kan wasu makudan kudade
Wasu 'yanbindiga sun yi rashin sa'ar samun Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba
An bayyana shirin rusa gidaje masu hadari a Abuja da cewa shiri ne na taimakon al'umma baki daya.
Kwararru sun lura cewa noma na iya kai arewacin Nijeriya ga gaci. To amma ana sako sako da bangaren na noma.
Takaddamar iko da jam'iyyar adawa ta APC ta bayyana karara bayan kaddamar da wata jami'a a Sakkwato da ta tara jiga jigan 'yan APC tun daga nesa amma Bafarawa bai je ba.
Domin Kari