Kungiyar Al-Shabab ta kai harin kunar bakin wake kuma har mutane 7 sun mutu
Rasha ta bukaci Amurka data sake nazari akan umurnin da bayar game da kulle wasu gine-ginen ta guda 3.
An nada mace a matsayin ministan tsaro a kasar India, Hakan ko ya biyo bayan garanbawul ne da Prime Ministan kasar Nerendra Modi yayi wa majilisar gudanarwansa.
Anyi hasarar dukiya mai tarin yawa a jihar Benue sakamakon ambaliyar da akayi, kuma ya shafi kananan hukumomi har 12.
Ana daf da fara dawo da Alhazan Najeriya, Alhazan ke fuskantar matsalolin iri daban-daban da suka hada da wurin kwana da kuma wurin kewaya wa.
Gwamnanjihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari yace yana goyon bayan sake fasalin Najeriya amma akwai abinda za ayi laakari dasu idan anzo yin hakan
Gwamnan jihar NigerAlhaji Abubakar Sani Bello yace bai dace a ajiye mutane gidan yari ba tare da yanke musu hukunci ba akan lokaci.Gwamnan yana magana ne sailin da ya ziyarci gidan yarin garin Kontagora
Masu lura da al'amura na yau da kullum na cewa ga dukkan alamu, har yanzu Korea ta arewa ba ta janye da barazanar da ta ke yi na harba makamai masu linazmi ba, inda a baya-bayan nan ta harba wani da sanyin safiyar yau Talata duk da takunkumin da ake kakaba mata.
Tituna a birnin Berkeley a jihar Califonia dake nan Amurka ya cika makil da dan mutun domin gudanar da zanga-zangar maida martani duk ko da kokarin hana wannan zanga-zangar
Kotu ta dakatar da umurnin shugaban kasar Guatamala
An kawo karshen kiki-kakan da ake yi game da zaben sarkin Dogon Dutse dake cikin jamhuriyar Niger.
Kungiyar maaikatan kanan hukumomi sun gudanar da 'yan kware-kwaren zanga-zanga zuwa majilisar dokokin jihar Niger domin neman majilisar tasa hannu a dokar da zata basu damar cin gashin kai
Yanzu haka Jamaa sun fara kokawa game da farashin ragunan layya, da yawan jamaa na cewa ko baya ga tashin farashin raguna haka kuma kudi sunyi wahalar samu.Hatta suma masu sayar da ragunan sun koka akan rashin kasuwa.
An bullo da tsarin ciyar da alhazan Najeria, sabanin yadda ake barin Alhaji ya nemi abinci da kansa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa 'yan kasar jawabi kan dabarun yadda zai tunkari yakin Afghanistan yayin da Amurkawan suka fara dasa alamar tambayar shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?
Shugaba Muhammadu Buhari Na Najeriya yayi jawabi ga 'yan kasa bayan ya dawo daga kasar Birtaniya inda ya kwashe sama da kwanaki 100 yana jinya, Ya bukaci 'yan kasar da suci gaba da hada domin ci gaban kasa.
'Yan kasar Hong KOng sunyi bore akan hukuncin da gwamnatin kasar ta yanke aka wasu mutane 3 masu rajin kare demokaradiyya.An yanke musu hukunci dauri ko biyo bayan rawart da suka taka na nuna kyamar gwamnati tun a shekarar 2014
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana rawar da Amurkja zata dauka a kasar Afghanistan kumawannan yana cikin jawabin da zai gabatar a daren littinbi.
Ana ci gaba da cece kuce akan sarautar dogon dutse dake cikin jamhuriyar Niger abinda wasu ke ganin ana son a take musu hakkin su abinda suka ce ba zasu yarda da hakan ba.
'Yan kasar Kamaru sun koka akan yadda ake samun yawan haduarin mota a kasar abinda suka ce kusan kullun mutane sama da 50 ne ke rasa rayukan su sakamakon hadarin mota
Domin Kari