Wani jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar adadin wadanda ke mutuwa sanadiyyar annonar COVID-19 a duniya ya kai miliyan biyu idan har ba a samu ingantacciyar allurar rigakafin cutar ba.
Amurka ta ce za ta ba yankin Sahel da ke Afirka wani sabon tallafin kudi na dala miliyan 152 domin tallafawa yankin wanda ya kasance daya daga cikin yankunan da ke fama da tarin rigingimu a duniya.
Sarkin masarautar Zazzau a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya mai martaba Alhaji Shehu Idris ya rasu. Ya rasu yana mai shekara 84.
Hukumar zabe a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ayyana gwamna Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben jihar.
Al’umar jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya sun dunguma zuwa rumfanan zabe a ranar Asabar domin zabo wanda zai shugabancin jihar har na tsawon shekara hudu.
Jami’an lafiya na yin gargadi ga jama’a, da su je su yi allurar rigakafin cutar nau’in murar nan da ake kira flu a turance, domin kaucewa yin fama da cutar COVID-19 da murar a lokaci guda.
Ana ci gaba da nuna alhini dangane da rasuwar Mai Shari’a a kotun kolin Amurka Justice Ruth Bader Ginsburg, wacce ta rasu a ranar Juma’a tana mai shekara 87.
Ma’aikatar harkokin kasuwancin Amurka ta ce za ta fitar da wani umurni a ranar Juma’a wanda zai hana jama’ar kasar sauke manhajojin WeChat da TikTok na kasar China.
A Najeriya, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obansajo wanda ke sukar lamirin gwamnati mai ci yayin da ita kuma take zargin sa da yunkurin rarraba kawunan 'yan Najeriya a martanin da ta mayar masa.
Bayan da suka kwashe wasu kwanaki cikin mawuyacin hali a kasar Girka an kwashe 'yan cirani da 'yan gudun hijira zuwa wani matsuguni bayan da sansanin da suke zaune ya yi gobara.
Jimullar wadanda cutar Coronavirus ta kama a sassan duniya na ci gaba da karuwa yayin da har yanzu Amurka, India da Brazil suka kasance kasashen da cutar ta fi kamari.
Wakilai daga yammacin Afirka karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, sun isa Bamako, babban birnin kasar Mali a ranar Asabar, a wani mataki na Neman maslaha ga rikicin siyasar kasar da ya kai ga wasu sojoji suka yi juyin mulki.
Gwamnatin Libya da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya, ta ayyana shirin tsagaita-wuta a duk fadin kasar, ta kuma yi kira da a dakatar da duk wasu ayyukan soji a birnin Sirte - matakin da majalisar dokokin bangaren ‘yan adawa ta amince da shi.
Yayin da sama da jami’an kashe gobara dubu 12 ke ta kokarin shawo kan wata wutar daji da ke ci a California da ke Amurka, gwamnan jihar Gavin Newsom ya ce, ya nemi taimakon kasashen Canada da Australia, baya ga tallafin da ya nema daga gwamnatin tarayya.
Wani jirgin sama dauke shugaban ‘yan adawar kasar Rasha Alexie Navalny wanda ba ya cikin hayyacinsa, bayan da aka yi zargin saka masa guba, ya sauka a Berlin a yau Asabar.
Kasar Malaysia, ta sassauta wasu ka’idoji da ta gindayawa ma’aikatun kasar wajen daukar baki a aiki.
Jakadan kasar Belarus a Slovakia, Igor Leshchenya, ya nuna goyon bayansa ga masu zanga zanga a wani faifain bidiyo da kafar yada labarai ta Nasha Niva ta Belarus ta wallafa a ranar Asabar, wanda ba a tantance ranar da aka nade shi ba.
Amurka da Korea ta Kudu za su fara atisayen soji na hadin gwiwa na shekara-shekara da suka saba yi a ranar Talata mai zuwa.
Domin Kari