Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Hushpuppi Da Hannu A Zambar Dala Dubu 400 Yayin Da Yake Tsare A Gidan Yari A Amurka - Jami'in FBI


Hushpuppi
Hushpuppi

Wani wakilin leken asiri na musamman, Andrew John Innocenti, dake aiki a karkashin hukumar binciken gwamnatin tarayya ta gwamnatin Amurka, ya yi zargin cewa fitaccen jarumin nan na Instagram Hushpuppi ya sake samun sabbin tuhume-tuhume.

Wannan na zuwa ne a yayin da masu gabatar da kara na Amurka suka mika takardun kotu da ke nuna cewa ya aikata zamba tare da karkatar da sama da dalar Amurka miliyan 400 a yayin da yake zaune a kurkukun kasar.

Kamar yadda rahotanni da dama daga Najeriya suka ruwaito, takardun da aka gabatar a gaban Kotun Gundumar Amurka ta California a ranar Laraba 16 ga Maris, 2022 sun nuna sabbin shaidun da ke nuna Hushpuppi na aikata zamba a gidan yarin na Amurka.

Takardun kotun sun bayyana cewa Hushpuppi, yayin da yake gidan gyaran hali na Tarayyar Amurka, ya shiga cikin saye da wanzar da katunan cirar kudi na Tasirin Tattalin Arziki da ake kira Economic Impact Payment debit cards ta hanyar yaudara da ake samu daga satar bayanan 'yan kasar Amurka da mazauna kasar.

Economic Impact Payment debit, tallafin kuɗi ne da gwamnatin Amurka ke bayarwa ga mazauna Amurka bisa ga Dokar CARES. Ɗaya daga cikin hanyoyin da mazauna Amurka wanda suka cancanta suke karɓar kudin, ta katunan zare kudi ne.

Daga cikin takardun da aka gabatar a kotu, an gano cewa masu satar bayanai na amfani da bayanan mazauna Amurka wajen turawa wa gwamnati don samun katunan cirar kudin. Suna sayar da waɗannan katunan EIP a boye ga sauran masu aikata laifukan yanar gizo.

Hukumomin Amurka sun ce duk da cewa fursunonin ba su da dan kalillan damar yin amfani da tarho, bidiyo, intanet, da kuma kamfuta saboda 'yancinsu na sirri don shigar da kara a kotu. Kamar sauran waɗanda aka tsare, an ba Hushpuppi damar shiga hanyar sadarwar kwamfuta kuma.

Sai dai, tsakanin 28 ga Janairu zuwa 4 ga Maris, 2022, hukumomin tsaro a gidan yarin tarayya a Amurka sun lura cewa Hushpuppi yana yawan amfani da intanet.

Sai aka saita masa tsarin bibiyan ayyukansa na kwanaki 7.

Daga nan ne aka gano cewa Hushpuppi yana sayan katunan zare kudi na EIP daga wata kasuwa mai aikata laifuka ta yanar gizo mai suna StimulusCard ("https://stimuluscard.com/").

XS
SM
MD
LG