Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Wanke Sojojin Najeriya Daga Zargin Cin Zarafin Bil Adama


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya ta wanke sojojin kasar daga zargin da kungiyar Amnesty Internatioanl ta yi na cewa sojojin Najeriya na take hakkin bil Adama.

A wani al’amari mai kama da martani ga kungiyar kare hakkin bil Adama ta Duniya Amnesty International, da a baya ta zargi sojojin Najeriya da cin zarafin bil Adama. Hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya ta wanke sojojin Najeriyar.

A cewar babbar sakataren hukumar ta Najeriya, Mrs Oti Ovrawah, tace hukumar na farin cikin fadin cewa rundunar sojan Najeriya ta na la’akari da muradun kare hakkin bil Adama, a duk yake-yaken da ta keyi da ‘yan ta’adda wanda ke da muhimmanci ga ‘yan Najeriya.

Tun da farko sai da babban hafsan sojan Najeriya, Janal Tukur Buratai, yace dakarun kasar basa wani rufa-rufa game dangane da batun kare hakkin bil Adama, inda ya ci gaba da cewa basu da wani abu da zasu boye, idan aka duba ganin cewa dokokin aikin soja suna kare Muradin ‘kasa da kuma kare dukiya da rayukan jama’a ne.

Zargin da kungiyar Amnesty International ta yi wa dakarun Najeriya, ya haifar da cece-kuce a cikin ‘kasar.

Darakta janal na hukumar wayar da kan jama’a ta Najeriya, Dakta Garba Abari, na ganin abubuwan da suka faru a kasar zai zamanto darasi ne ga kungiyar Amnesty International.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG