Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Da Kungiyoyi Sun Himmatu Wajen Kare Hakkokin Kananan Yara


A Najeriya fafatukar da hukumomi da kungiyoyi ke yi na kare hakkokin kananan yara na kara habaka domin an soma samarda dokokin da zasu kare hakkin yaran da ma basu zo duniya ba.

Wannan yana zuwa ne lokacin da Jihohin kasar ke ta yin kwaskwarima ga dokokin kare hakkin yara na kasar, domin aiwatarwa a Jihohin su.

Tun shekarar 2003 lokacin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ne aka rattaba hannu ga daftarin dokokin kare hakkokin kananan yara, sai dai yau kimanin shekaru goma sha takwas kenan Jihohi, musamman na arewacin kasar basu kammala yin kwaskwarima ga dokokin ba balle aiwatarwa a Jihohin su.

Wannan a cewar wakilin majalisar duniya a Najeriya Edward Kallon, bai rasa nasaba da yanayin fahimtar da jama'a ke da shi.

Ya bayyana cewa, “Wasu daga cikin kalubalen dake tarnaki ga hakan sune na fahimta, inda jama'a ke alakanta al'adu da addini ga kula da yara har girman su, suna ganin kamar an cusa musu akidun turawa abinda kan iya sa su hinjire domin suna ganin sun san hakkin su. Akan haka ne ma nake taya Sakkwato murna akan samun nasarar yin aiki tukuru wajen hada hankula wuri daya da samun daidaito har aka amince da dokar a jihar”.

Kafin samar da dokar a Jihohi ana ta samun matsalolin cin zarafin kananan yara ta nau'o'i daban daban, amma wannan dokar da gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya saka hannu ya ce zata yi tasiri wajen kawo karshen wadannan matsalolin.

Kafin jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya ta yi kwaskwarima da saka hannu ga dokokin kare hakkokin kananan yara, wasu Jihohi tuni suka kai ga wannan matakin, to amma gwamnatin tace nata dokokin sune mafi inganci a cewar babban Lauyan Najeriya Sulaiman Usman wanda shine babban lauyan gwamnatin jihar ta Sakkwato.

Duba da cewa kafin wannan lokacin akwai daruruwan matsalolin cin zarafin kananan yara da aka samu, wasu na gaban kotuna ana ta shara'a, yanzu samar da wannan daftarin dokar mai yiwuwa ya sauwaka wadannan matsalolin a cewar Rabi'u Bello Ghandi na kungiyar kare hakkin yara da ake kira "save the child initiative."

Shekaru 18 da sa hannu ga daftarin dokokin kare hakkokin kananan yara a Najeriya har yanzu Jihohi 10 na arewacin kasar basu samar da dokokin a Jihohin su ba balle su soma aiki abinda kan iya nuna cewa har yanzu da sauran rina a kaba.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00


XS
SM
MD
LG