Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kenya: Rufe Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Dadaab Ya Sabawa Doka


Sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab.
Sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab.

Babbar kotun Kenya ta ba da sanarwar cewar kada gwamnati ta rufe sansanin ‘yan gudun hijira nan na Dadaab, saboda yin haka ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Tun cikin watan Mayun bara ne ake wannan ikrarin rufe sansanin, lokacin da gwamnati ta ba da sanarwar za ta rika mayar da ‘yan gudun hijira Somalia zuwa kasarsu ta Somalia kafin karshen watan Nuwamban 2016 kuma ta sa hukumar yan gudun hijiran kasar ta wargaza shirin.

Kenya ta ce wannan mataki na ta ya zama tilas ne sakamakon barazanan tsaro.

Wani alkali a babban kotun Kenya JM Mativo ya zartar da hukunci cewar wannan umarnin gwamnati na nuna bambanci kuma ya kai ga a aiwatar da hukunci.

Dadaab shine sansanin yan gudun hijira mafi girma a fadin duniya kuma ya na daukar mutane dubu dari uku wanda akasarinsu yan kasar Somalia ne.

Kalubalantar shawarar gwamnatin na rufe sansanin yan gudun hijiran na Dadaab da hukumar yan gudun hijirar kasar ya biyo bayan karar da wasu kungiyoyin Kenya masu rajin kare hakkin bil adama guda biyu suka kai a kotu.

Sai dai gwamnatin Kenya ba ta gaggauata mayar da martani a kan wannan hukuncin kotun ba.

XS
SM
MD
LG