Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makomar Nahiyar Afirka Idan Sabon Shugaban Amurka Ya Dare Mulki


Biyo bayan jawabin da sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump yayiwa magoya bayansa a hedikwatar gangamin yakin neman zabensa da ke birnin New York.

Wasu ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu game da wannan jawabi da zabebben shugaban yayi, musamman ma irin fahimtar da suka yiwa jawabin.

Zaben sabon shugaban Amurka Donald Trump zai taimaka wajen daga darajar Naira a kasuwannin duniya inji wasu ‘yan Najeriya dake ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan makomar kasar da kuma nahiyar Afrika biyo bayan nasarar da ya samu - inji wani mai fashin baki kan harkokin siyasa da na difilomasiyya Dr, Umar Ardo.

A daya bangaren kuma ra’ayoyin sun bambanta inda su Alhaji Mafindi da Alhaji Kabiru Marafa ke kallon cewa ba Najeriya kawai ba hatta nahiyar Afrika, zata fuskanci mawuyacin halin ta fuskar difilomasiyya da na tattalin arziki saboda a cewarsu ko da an sami canji ta fannin shugabanci, manufofin kasar Amurka ba zasu sauya ba.

Da yake fadin albarkacin bakinsa tsohon gwamnan jihar Gongola a jumhuriya ta biyu, Ambasada Wilberforce Juta, ya ce akwai alamu Donald Trump ya sanya salo, idan aka kwatanta da irin zazzafar kalaman da ya rika yi lokacin yakin neman zabe.

Abin jira a ganin yanzu shine irin kamun ludayin salon mulki na sabon shugaban, bayan ya dauki rantsuwar kama aiki a watan Janairun shekara ta 2017, a matsayin shugaban Amurka na 45.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG