Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin Wasu Mazauna Yankin Niger Delta Kan Sakamakon Zaben Amurka


Donald Trump
Donald Trump

Zaben kasar Amurka da kuma sakamakon zaben da ya biyo baya, wani al’amarine da ya dauki hankalin duniya baki daya.

A Najeriya, al’umomin yakin Niger Delta da mazauna yankin ba a barsu a baya ba wajen bayyana ra’yoyinsu. Kamar yadda wani mazaunin yankin ke cewa Amurkawa sun riga sun zabi mutumin da suke so ya shugabance su Mr. Donald Trump, sabanin yadda ‘yan Najeriya ke tunani.

Ita kuma Gloria Micheal, cewa tayi a nata ra’ayin taso ace ‘yar uwarta mace ce ta lashe zaben Amurka, wanda yaci zaben Amurka mutum ne mai nasara. Shima Ugochukwu, cewa abin da ya faru a Amurka, shine Amurkawa ke so.

Sidi A Sidi, yayi fatan alkhairi ga sakamakon zaben Amurka, inda yace Allah yasa wannan ya zama alkhairi ga musulunci da Musulmai a duniya. Sai dai kuma Alhaji Umaru na ganin Amurka da sauran kasashen duniya suna cikin matsala, domin wasu tsatstsaucin ra’ayinsa da ya yada lokacin yakin neman zabe.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

XS
SM
MD
LG