Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Papa Roman Ya Zaiyarci Kasashen Larabawa


Papa Roman Francis da Sheikh Ahmed Mohamed el-Tayeb, babban limamin Azhar ta Misra.
Papa Roman Francis da Sheikh Ahmed Mohamed el-Tayeb, babban limamin Azhar ta Misra.

Shugaban mujami’ar katolika na duniya Papa Roman Francis ya kai ziyara ta farko da babu wani Papa Roman da ya taba yi a yankin kasashen Larabawa inda addinin Musulunci ya samo asali.

Francis ya fara yada zango ne a Hadaddiyar Daular Larabawa a yau Lahadi inda zai halarci wani taron addinai. Zai dai koma Rum ne a ranar Talata.

Kafin ya bar fadar Katolika ta Vatican, Francis yace yana lura da matsalolin taimako da ake fama dasu a kasar Yamal cikin damuwa, ya kuma yi kira ga bangarori masu fada su mutunta yarjejeniyoyin kasa da kasa da aka cimma kuma su bada dama a shiga da kayan abinci ga Yamanawa.

Papa Roman Francis da babban limamin jami’ar Azhar ta Mirsa inda Sunni ta kai shekaru dubu a wurin Sheikh Ashamed el-Tayeb zasu yi jawabi a gobe Litinin a wurin wani taron hadin kan bil adama. Wadanda zasu halarci taron sun hada da Musulmi da Krista da Yahudawa da mabiya addinan Hindu da Buddhist da wasu addinan.

Taron da halartan Papa Roman duk wani yunkuri ne da Hadaddiyar Daular Larabawan ke yi na hada kan addinai, lamarin da ta yiwa take shekarar hadin kai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG