Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Da Wasu Kasashen Turai Sun Bukaci A Gudanar da Sabon Zabe A Venezuela


Venezuela Political Crisis
Venezuela Political Crisis

Kasashen Birtaniya da Spain da Faransa, da Sweden da kuma Denmark sun bayyana amincersu ga shugaban ‘yan adawan Venezuela a matsayin shugaban kasa mai riko.

Kasashen na Turai suna bukatar Venezuela ta gudanar da wani sabon zaben shugaban kasa nan bada dadewa ba domin kawo karshen rikicin siyasa da matsalolin kayan taimako.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt ya dora a shafinsa na Twitter cewa Nicholas Maduro bai bayyanar da sakamakon zaben shugaban kasa tsakanin kwanaki takwas da doka ta gindaya ba. Yace a don haka Birtaniya da kawayenta na Turai sun amince da Juan Guaido a matsayin shugaban kasa bisa tsarin doka, har kafin a gudanar da zaben gaskiya. Yace da fatar wannan mataki zai kai ga kawo karshen bukatar kayan taimako.

Firai ministan Spaina ya fada a ranar Litinin a birnin Madrid cewa suna aiki ne domin maido da cikakken tsarin demokaradiya a Venezuela.

A wani jawabi ta telbijin harshen Spanish a jiya Lahadi, Maduro yace ba zasu amince da wa’adi da wani zai gindaya musu ba. Yace tamkar shi ne yake baiwa kungiyar Tarayyar Turai kwanaki bakwai ta amince da kafa kasar Catalonia in ba haka ba zai dau mataki. Yace babu siyasar kasa da kasa da ake yi bisa sharadi da wani zai gindaya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG