Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Albashi Ya Jefa Ma’aikatan Kogi Cikin Wani Hali


File photo
File photo

Ma’aikatan gwamnatin jihar Kogi dake tarayyar Najeriya sun kwashe watanni 12 ba tare da an biya su albashinsu ba.

Sakamakon share watanni 12 ba tare da albashi ba, ma’aikatan jihar Kogi sun shiga wani mawuyacin hali. Ranar Alhamis din da ta gabata ne kungiyar Kwadago jihar ta dawo daga yajin aikin na kwanaki uku domin yin gargadi ga gwamnatin jihar.

Shugaban kungiyar Kwadagon jihar Kogi, Kwamred Onu Edoka, yace kimanin ma’aikatan gwamnati 450 ne suka mutu, sakamakon tashin hankalin da suka shiga na rashin biyan albashi. Sai dai kuma gwamnatin jihar tace aikin tantance ma’aikatan bogi ne yasa aka samu jinkirin biyan albashin.

Kamar yadda wasu daga cikin ma’aikatan suka bayyanawa Muryar Amurka, akwai ma’aikatan jihar da suka kwashe sama da shekara guda ba tare da samun albashin ba, inda kuma su kayi kira ga gwamnan jihar da ya taimaka ya biya albashi cikin gaggawa.

Kamar yadda gwamnatin jihar Kogi tace hakan ya faru ne sakamakon aikin tantance ma’aikatan bogi ne, domin magance matsalar cin hanci da yayi katutu a tsakanin ma’aikatan jihar.

Daraktan cibiyar samar da bayanai Abdulkareem Abdulmalik, yace ya zuwa yanzu sun sami ci gaba a aikin tantance ma’aikatan, inda yace sun bankado ma’aikatan bogi dubu 18 ciki har da masu yin aiki daga kasashen waje.

Kungiyar kwadagon jihar ta baiwa gwamnatin jihar wa’adin makonni biyu masu zuwa da a biya dukkan ma’aikatan ko kuma a koma yajin aiki har sai abin da hali yayi.

Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG