Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sababbin Kudurorin Amurka Kan Nahiyar Afirka


Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00

Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken a Najeriya.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yaye kallabin sababbin kudurorin Amurka sa'adda yake jawabi ga jami'an diflomasiyya da na gwamnatoci a sakatariyar kungiyar raya kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS a Abuja, babban birnin Najeriya, inda ya ke ci gaba da ziyara

A can baya manyan kasashen da suka ci gaba a duniya, na kallon kasashe masu tasowa musamman na nahiyar Afirka a zaman cima-kwance.

Manazarta na gani suma wasu kasashen masu tasowa sun rungumi wannan tunani, na cewa tilas su dogara kacokam kan kasashen da suka ci gaba domin wanzuwarsu.

To sai dai gwamnatin Amurka ta sauya tunani akan wannan lamari, kamar yadda sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya bayyana, a yayin da yake jawabi kan manufofi da tsare-tsaren Amurka ga nahiyar Afirka.

Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken A Najeriya
Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken A Najeriya

Ya ce an kwashe tsawon lokaci ana daukar kasashen Afirka a matsayin kananan abokan hulda, a maimakon dangataka ta tsara. Sau tari mukan nemi kasashe abokan huldarmu da su bi ko su goyi bayan wani tsari na kasa-da-kasa, wanda ba inda zai amfani bukatun al’ummarsu.

Akan haka ya ce lokaci yayi, da Amurka za ta kawo sauyi a wannan tsarin, na hulda da dangantaka da kasashe musamman na nahiyar Afirka mai kasashe 54 da kuma ke zaman muhimmin yanki na habakar tattalin arziki a duniya.

Ya ce "ina son tabbatar da cewa Amurka, ba ta bukatar takaita kawancenta da wasu kasashe, muna son hadin gwiwar mu da ku ta yi karfi. Ba ma bukatar tilasta muku yin zabi, sai dai mu ba ku damar bin zabin da kuke so. Idan muka hada karfi tare, za mu samar da amfani mai yawa ga jama’armu. Amurka tayi amanna cewa, lokaci yayi da za’a daina batun Afirka a matsayin siyasar yanki, DOMIN a soma daukarta a matsayin muhimmin yankin siyasa na duniya da take da shi."

Kawancen na Amurka da kasashen Afirka dai zai maida hankali ne akan muhimman abubuwa 5, da suka hada da sauyin yanayi, karfafa tattalin arziki, inganta tsarin dimokaradiyya, sha’anin tsaro da kuma kiwon lafiyar duniya, musamman yaki da annobar coronavirus.

Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken A Najeriya
Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken A Najeriya

Sakatare Blinken ya ce ba yadda za’a yi a cimma wadannan bukatun na duniya ba tare da hadin kan nahiyar Afirka ba.

Haka kuma ya bayyana irin baiwa da karfi da nahiyar take da su, ciki har da samuwar kasa irin Najeriya.

Ya ce karfin Afirka yana tattare a cikin Najeriya, saboda kasar sai kara habaka take yi. Ga ta da kakkarfan tsarin dimokaradiyya, da karfin tattalin arziki, sannan kuma da al’umma masu jini a jika.

Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken A Najeriya
Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken A Najeriya

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, wanda kuma shine shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP a Najeriya, na daga cikin wadanda suka sahidi jawabin na Sakatare Blinken.

Taron ya sami halartar manyan jami’an difilomasiyyar kasashen Afirka, da wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya, da kuma shugabannin kungiyoyin farar hula.

Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken A Najeriya
Ziyarar Sakataren gwamnatin Amurka Anthony Blinken A Najeriya

amurka-za-ta-taimakawa-najeriya-shawo-kan-matsalar-tsaro-da-cin-hanci-da-rashawa

amurka-ta-cire-najeriya-daga-cikin-kasashe-masu-take-yancin-addini

Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna cikin sauti:

Sababbin Kudurorin Amurka Kan Nahiyar Afrika
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG