Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kudu Ta Cika Shekar 10 Da Samun Yanci Kai


Sudan Ta Kudu
Sudan Ta Kudu

Sudan ta Kudu ta cika shekara 10 da samun yanci kai yau Jumma’a sai dai babu wani abin kirki da za a yi murna a kasar da yakin basasa ya durkusar inda ake fama da rashin kwanciyar hankali na yau da kullum da kuma matsananciyar yunwa.

A tsakiyar daren ranar 9 ga watan Yulin 2011, shagulgulan biki ya barke yayin da aka haifi sabuwar kasar a duniya kuma mutanan Sudan ta Kudu sun yi murnar ganin karshen gwagwarmayar shekara goma na neman kasa daga Sudan.

Bayan Shekaru biyu, Sudan ta Kudu ta kasance cikin yaki, aka manta da aikin gina kasa, yayin da wadanda suka yantar daita suka wargaza kasar, wanda suka yi fatali da babban cigaban da ake fata na samun zaman lafiya da ci gaba a nan gaba.

Kusan mutum dubu 400,000 ne suka mutu kafin a ayyana tsagaita wuta a 2018, amma kasar ta yi ta fadi tashi don hadewa kuma yafi rauni fiye da ko wane lokaci da fuskantar yunwa da rashin tsaro na siyasa da lalacewar tattalin arziki da kuma bala’o’i na kasa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG