Kungiyar ta kara da cewa za su yanke huldar diflomasiyya da kuma sanya takunkumin tattalin arziki mai tsauri, saboda jinkirin da kasa ta yi na gudanar da zabuka, abinda ba za'a amince da shi ba, bayan juyin mulkin da soja suka yi a shekarar 2020.
Sabbin matakan da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta dauka na nuna tsananta matsayinta akan kasar Mali, bayanda hukumomin wucin gadi suka bayar da shawarar gudanar da zabe a watan Disamba na shekarar 2025 maimakon wannan watan Fabrairu na wannan shekarar kamar yadda kungiyar ta amince da farko.
A cikin sanarwar da ta fitar bayan wani taron gaggawa da aka yi a Accra babban birnin Ghana, ECOWAS ta ce ba za ta amince da jadawalin da aka tsara na komawa kan tsarin mulkin kasar ba kwata-kwata.
ECOWAS ta kara da cewa, wannan jadawalin "yana nufin gwamnatin rikon kwarya ta soja na shirin yin garkuwa da al'ummar Mali."
Kungiyar ta ce ta amince da sanya wasu karin takunkumai cikin gaggawa. Wadannan sun hada da rufe hanyoyin kasa da na sama na iyakokinsu da kasar Mali, da dakatar da hada-hadar kudade da ba su da mahimmanci, rike kadarorin gwamnatin Mali dake a bankunan kasuwanci na ECOWAS da kuma maido da jakadunsu dake Bamako gida.
A halin da ake ciki kuma, kungiyar hada-hadar kudi ta yankin UEMOA ta umurci dukkanin cibiyoyin hada-hadar kudi da ke karkashinta da su dakatar da kasar Mali ba tare da bata lokaci ba, tare da katse hanyoyin da kasar ke samu a kasuwannin hada-hadar kudi na yankin.
Gwamnatin rikon kwarya ta Mali ta ce ta yi mamakin wannan hukunci. A martanin da ta mayar, ta sha alwashin ita ma za ta rufe iyakokinta da kasashen na ECOWAS, da kuma kiran jakadunta su dawo gida da kuma sake nazari gamade kasancewarta mamba a ECOWAS da UEMOA.
“Gwamnati ta yi kakkausar suka kan wadannan matakan da aka kakaba, ba bisa ka’ida ba,” in ji sanarwar da mai magana da yawun gwamnatin, Abdoulaye Maiga ya karanta a gidan talabijin na kasar a safiyar ranar Litinin, inda gwamnatin ta yi kira ga ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu.
A baya dai hukumomin na Mali sun dora alhakin jinkirin zaben a kan kalubalan shirya zabe mai inganci yayinda ake fama da tashin hankalin 'yan kishin Islama.
-Reuters