Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga sun sace mutane a Jihar Adamawa


Rahotanni daga jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da jama’a sun kai farmaki a wasu garuruwa biyu a jihar da suka hada da Ngwalam da kuma mararraban Jada,inda suka yi awon gaba da wasu yan kasuwa domin neman kudin fansa.

Bayanai sun nuna cewa masu garkuwar sun kai farmaki ne a garin Ngwalam dake yankin Numan, a cikin dare inda suka yi awon gaba da iyalan wani dan kasuwa, wanda ya zuwa yanzu ba’a ji duriyarsu ba, kamar yadda wani mazaunin garin ya shaidawa muryar Amurka a safiyar wannan jumma’a.

Kawo yanzu rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, bata yi karin haske ba tukunna akan sace wadannan mutanen, to amma kuma a kullum hukumomin tsaro sukan ce suna nasu kokari domin dakile wannan matsalar ganin cewa lamarin sai kara ta’azzara yake yi a jihar.

Suleiman Baba dake zama jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron farin kaya ta sibil defense a jihar yace sun tashi tsaye.

Ko a makwanni uku da suka gabata ma sai da masu garkuwar suka sace wasu malaman jami’a biyu da kuma wani basarake a jihar.

ga karin bayani cikin sauti daga Ibrahim Abdul'aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG