Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Raji A Najeriya Sun Ce Sabon Shirin Bankin CBN Kan Sadarwa Zai Kara Matsa Ma Talakawa


CBN
CBN

Kungiyoyin jama’a sun yi fatali da sabon tsarin biyan kudi na N6.98 da masu amfani da wayar hannu ko konfuta za su rika yi, wanda bankin CBN da Hukumar Sadarwa ta Kasa su ka bullo da shi.

Daraktan wata kungiyar rajin kare muhalli mai suna Mother Earth Foundation, Arc Nnimmo Bassey, ya ce “tashin farashin mai cikin gida da shawarar da Babban Bankin ya yanke na bai wa bankunan ‘yan kasuwa damar karbar kudin amfani da hanyar sadarwar na N6.98, wani sabon salo ne na takura talakawa da marasa galihu irin na rashin imani.

Wannan shiri ne da ya kamata a bar shi inda aka tattauna amma bai kamata a fito da shi ba. Mutane na fama da tsadar rayuwa da kuma albashi mara tsoka, dan haka duk wata dawainiya a kan aljihun mutane, koda na kwabo ne, zai zama babbar takura.

Ya yi kira ga CBN ya janye wannan shiri. Za su iya cajin manyan kudi da miliyoyi da biliyoyi a kan duk wani aiki. Akwai fa iyakar da Babban Bankin zai iya tura ‘yan kasa ga bango. Su na so ‘yan Najeriya su fara tara kudadensu a karkashin filo ne. CBN ya daina takurawa talakawan Najeriya.

Shugaban wata kungiyar rajin kare hakkin bil Adama ta, Global Rights, Abiodun Bayewu, ya ce “Wannan fashi da makami ne da rana tsaka.” Tattalin arziki ya riga da ya tabarbare kana yanzu ne kuma ake bullo da wani abin da zai kara tsadar rayuwa ne?

“Za mu iya tunanin yiwuwar a fuskanci koma baya a yunkurin mu na kafa tattalin arziki mara amfani da tsabar kudi, tun da yake ba a nuna tausayi ba.”

Ya ce “Ba wai lokacin da aka bullo da shirin ne kadai bai dace ba, wannan rashin imani ne da aka kawo domin gallaza wa ‘yan kasa a wannan lokaci.”

Abiodun ya yi kira da a gaggauta janye wannan shiri saboda lokacin bai dace ba kana babu wani taimako da zai yi wa tattalin arzikin mutane da dama.

XS
SM
MD
LG