Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaman Lafiya Ya Soma Dawowa a Kasar Burkina Faso


Shugaba Michel Kafando wanda yanzu ya koma kan mulkin kasar Burkina Faso

Biyo bayan mayarda gwamnatin Michael Kafando kan karagar mulkin kasar Burkina Faso yanzu zaman lafiya ya soma dawowa kasar da wasu sojoji suka yiwa juyin mulki makon jiya

Shugabannin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ko ECOWAS su suka yi tattaki zuwa Burkina Faso suka matsawa shugaban sojojin da suka yi juyin mulki lashe aman da suka yi.

Shugaban rikon wucin gadi Michael Kafando ya koma kan karagar mulki lamarin da yanzu ya soma kwantar da hankulan 'yan kasar da suka shiga zanga zangar kin jinin sojojin.

Babban birnin kasar Ouagadougou ya soma samun kwanciyar hankali yayinda sojoji da 'yansanda suka kwashe tankunan yakinsu suna komawa barikinsu ganin cewa wadanda suka yi juyin mulkin sun kwashe nasu inasu daga fadar gwamnati da suka mamaye.

Bankuna da kasuwanni da ada suka rufe kofunansu yanzu sun soma budewa.

Wani mazaunin birnin Kafanda Haruna yace rayuwa ta yi masu wuya cikin dan lokacin da sojoji suke rike da mulki. Yace da kyar mutum ya samu cimaka ya saya a kasuwa. Yace sun sha wuya ainun.

Kazalika gidajen man fetur ma sun kara kashi hamsin kan farashinsu saboda karancin man. Saidai ana kyautata zaton wasu gidajen man zasu bude yau Juma'a

Har yanzu dandalin dake tsakiyar garin na rufe saboda haka musulman da suka so su yi sallah a dandalin jiya Alhamis kamar yadda aka saba dole suka hakura da zuwa filin kwallon wasa inda suka yi salla.

Dauda Birba da ya je sallah a filin kwallon yace ya yi murna Shugaba Michael Kafando ya koma kan mulki. Yace makon jiya basu yi aiki ba kuma basu iya fita ba sabili da rikicin. Amma yace da yaddar Allah nan da 'yan kwanaki kadan za'a fara aiki gadan gadan ba tare da wata matsala ba.

A wani halin kuma Janar Gilbert Diendere da ya jagoranci juyin mulkin yace ya yi nadama da abun da ya yi musamman idan aka yi la'akari da cewa sanadiyar rikicin har mutane goma sun rasa rayukansu.

Duk da cewa sojojin da suka yi juyin mulki masu kare fadar shugaban kasa sun ajiye makamansu wani Amadou Traore yace yin hakan bai isa ba. Yana bukatar a wargazasu. Yace bama son mu sake jin duriyarsu domin sun kashe 'yanuwansu.

Kawo yanzu dai ita gwamnatin da ta koma kan mulki bata bayyana abun da zata yi da sojojin ba. Haka ma bata ce komi ba akan zaben da ta shirya zata yi ranar 11 ga watan Oktoba kafin sojojin su katse mata hanzari.

XS
SM
MD
LG