Accessibility links

​Daruruwan mata ne sukayi zanga-zangar lumana da maracen jiya a Kano dangane da abin da suka kira halin ko in kula da gwamnatin Tarayyar Najeriya ke yiwa batun ‘yan mata 234 da ‘yan bindiga suka sace a kwalejin ‘yan mata ta garin Chibok na jihar Borno fiye da makonni biyu da suka gabata.

Matan wadanda ke karkashin inuwar gamayyar kungiyoyin sa kai dana fararen hula, musamman masu fafutukar kare hakkin bil adama dake Kano, wadanda suka kunshi mata da maza.

Masu zanga-zangar wadanda ke sanye da bakaken kaya domin tabbatar da halin alhini da zulumi da iyaye ke ciki, sun kunshi tsofaffi, matasa da ‘yan mata, kuma sun fitone daga kabilu, da sassa daban-daban na Najeriya.

Wannan masu zanga-zanga sun taka zuwa gidan gwamnatin Kano, inda suka mika wata wasika ga gwamnan na Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda suka ce lallai ya mika ta ga shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Mallam Bala Abdullahi, wanda shine shugaban kungiyoyin kare hakkin bil-adama a Kano, shine ya mika wasikar zuwa ga gwamna Kwankwaso.

“Muna so mu ja hankalin gwamantin Tarayya, da kuma al-ummar kasa baki daya, wato irin rikon sakainar kashi da akewa harkar tsaro, musamman ma abubuwan da suka jibanci satar yara da akayi, 234 a garin Cibok a Jihar Borno, yau kwana 16 kennan, ba’a gano inda yarannan suke ba, kuma babu wani cikakken bayani da zai gamsar da iyayensu,” a cewar Mallam Bala.

Mr. Abdullahi ya cigaba da cewa “shiyasa muka zo wajen gwamna, domin ya isar mana da sakonmu ga shugaban kasa, na irin bacin ranmu da kuma alhinin da muka samu kanmu a ciki”.

Hajiya Amina Hanga, itace ta jagoranci rukunin mata na masu zanga-zangar.

“So muke a dawo mana da ‘ya’yanmu. A dawo mana da yarannan. Hankalinmu a tashe yake, shiyasa yau muka saka bakaken kaya. Yanzu ana gaya mana cewa yarannan basa kasarnan, an fitar dasu waje. Anyi musu aure. Ana haka ne? A dawo mana da ‘ya’yanmu. Abunda muke rokon gwamnati kennan, kuma ba yau kadai za’a yi ba. InshaAllah zamu cigaba har sai ranar da aka dawo mana da ‘ya’yanmu,” a cewar Hajiya Hanga, tana magana muryarta na rawa.

Wata mata da ta hallarci taron sun nuna takaicinta ga lamarin Cibok “saboda rashin sanin dan adam, yau kwanaki 16 ba’a bamu cikakken bayani akan inda suke ba.
XS
SM
MD
LG