Yayin da duniya ke tsammanin an kama hanyar rabuwa da makamin nukiliyar Koriya Ta Arewa mai raunin tattalin arziki, sai ga shi Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo na gargadin cewa akwai sauran rina a kaba.
Hulda tsakanin kasashen Habasha da Eritiriya sai kara inganta ta ke yi. Ko a karshen makon nan, sai da shi ma Shugaban Eritiriya ya kai ziyara kasar Habasha, inda zai yi kwanaki uku ya kuma bude ofishin jakadancin kasarsa.
Ga dukkan alamu dai mahara sun sha alwashin sa kasar Somaliya gaba. Ko a jiya Asabar sai da su ka yi yinkurin sake yin kashe-kashe a wannan galabaitacciyar kasar, to sai dai Allah bai ba su nasara ba. A maimakon haka ma, an hallaka dukkanninsu biyar; su kuwa soja daya ne kawai su ka hallakar.
Yayin da zargin katsalandan din Rasha a zaben Amurka ke kara janyo takaddamar siyasa a cikin Amurkar, Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin tinkarar Shugaban Rasha muddun su ka yi tozali a Helsinki.
Yayin da wasu ke tsammanin wannan karon Shugaba Paul Biya zai yar da kwallon mangoron saboda shekaru, sai ga shi kuma ya ce zai sake tsayawa takara.
Bayan da kafafen yada labaran Burtaniya su ka yi ta yada labarin da ya samo asali daga jaridar The Sun ta Burtaniyar, cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki Firaminista Theresa May
Zamantakewar Jama'a
Ga dukkan alamu har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da kawo karshen nukiliyar Koriya Ta Arewa.
Yayin da ruwan sama kamar da bakin kwarya ke barazana ga kokarin da ake yi na ceto matasan nan guda 12,
Mugunyar kungiyar nan ta Taliban ta sake kai wani hari a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, inda su ka kashe mutane da dama
A wani al'amari da ka girgiza hanjin manyan baraye a fadin duniya, kotu ta zartas da hukuncin daurin shekaru 10 ga tsohon Firaministan Pakistan
Ga dukkan alamu rayuwar yaran nan da su ka makale cikin kogo mai cike da ruwa na fuskantar hadari yayin da tsarin ceto su ke dada kasancewa da sarkakkiya
Ga dukkan alamu an fara yaki tsakanin Amurka da China a fagen kasuwanci saboda rige-rigen sa haraji ma juna da su ke yi.
Zamantakewar jama'a
Yayin da wasu kwararru ke kaffa-kaffa da takardar kudin China, wasu kasashen Afirka na tunanin fara ajiyarsu ta kasashen waje a takardar kudin Chinar.
Da alamar dai ta leko ta koma ga yarjajjeniyar zaman lafiyar da aka cimma tsakanin Shugaba Salva Kiir na Sudan Ta Kudu da 'yan tawaye.
yayin da duniya ke farincikin alkawarin yin watsi da makaman nukiliya da Koriya Ta Arewa ta yi, sai kuma ga shi wata kungiyar na waswasin hakan.
Yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke shrin nada babban alkalin kotun kolin Amurka, har an fara karce kasa tsakanin 'yan ra'ayin rikau da 'yan gaba-dai gaba-dai
A cigaba da nuna rashin amincewa da manufofin Shugaba Trump kan shigowar baki, kungiyoyin magoya bayan kaurar jama'a daga kasa zuwa kasa za su yi zanga-zanga yau a fadin Amurka.
A wata babbar barazana ga kungiyar kasashen yankin Sahel biyar da ake kira G5, wasu 'yan bindiga sun kai hari a hedikwatarsu da ke Mali, inda aka yi jina-jina.
Domin Kari