A cigaba da sauye-sauye da Shugaban Amurka Donald Trump ke yi a bangaren shigi-da-fici, yanzu za a rika tsare mata bakin haure masu ciki.
A cigaba da dambarwar diflomasiyya da ake yi tsakanin Amurka da wasu kasashe 20 a gefe guda da kuma Rasha a daya gefen, Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha ta kira jakadun wasu kasashen don bayyana rashin jin dadinta.
Tana kasa ta na dabo game da batun farauto 'yan bindigar nan shida da su ka bace bat yayin da su ke tsare hannun 'yansandan jahar Kogi saboda wani rikici mai nasaba da Sanata Dino Melaye.
Ga dukkan alamu birni mafi cinkoso a Afurka, wato cibiyar kasuwancin Najeriya, Ikko zai dan sarara nan ba da dadewa ba, saboda samar da wasu manyan tasoshin mota da jiragen ruwa na zamani.
Zamantakewar Jama'a
A wani al'amari da hukumomi ke fassarawa da aikin ta'addanci, wani matashi ya kashe mutane biyu daga cikin wadanda ya yi garkuwa da su kafin daga baya jami'an tsaro su ka zagaye babbar kasuwar zamanin da ya yi garkuwa da mutane.
Kamar yaddsa aka zata kasar China ta mai da martani nan take bayan da Amurka ta saka haraji kan dinbin kayanta da ta ke shigo da su Amurka.
Bayan korafe-korafe da kuma fargabar yiwuwar a shiga kazamar gasar cinakayya tsakanin wasu kasashe da Amurka, yanzu Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce za a tsame wasu kasashe daga jerin masu biyan harajin kayan sayarwa.
Yayin da ake cigaba da murnar sakin akasarin 'yan matan Dapchi da kuma juyayin rasuwar biyar daga cikinsu, Shugaba Buhari ya sha alwashin ceto yarinya guda da ta rage a hannun 'yan Boko Haram.
Kubutattun 'yan matan Dapchi da iyayensu da 'yan'uwa da abokan arziki da jami'an gwamnati da sauran masu fada a ji na cike da farin cikin sakin akasarin 'yan matan Dapchi da kungiyar Boko Haram ta yi. To amma kuma wasu 'iyayen na bakin cikin mutuwar 'ya'yansu.
Yayin da ake hidimomin zagayowar Ranar Ruwa ta duniya, shakka babu wannan zai kuma sa a tuna da irin wahalhalun da ake fama da su a kasashe masu tasowa wajen batun samo ruwa da kuma tattalinsa
A wani al'amari mai ban jimami, dubban farar hula na gudu su na barin yankin Ghouta duk kuwa da yarjajjeniyar zaman lafiyar da aka ce an cimma kwanaki.
Da alamar za a bude wani sabon babi a rikicin Amurka da Rasha bayan da Rasha ta mai da martani saboda takunkumin da Amurka ta kakaba ma ta.
Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kashedi ga Sudan Ta Kudu game da bukatar tabbatar da zaman lafiya, Majalisar ta kuma kara tsawon wa'adinta a kasar.
Batun tabbatar da tsaro a Najeriya ya dau wani sabon salo bayan da Shugaban Najeriya ya gayyaci Sufeto-Janar na 'yansandan kasar don bayyana dalilinsa na kasa cigaba da zama a Binuwai kamar yadda aka umurce shi.
Da alamar za a shiga wata sabuwar rigima tsakanin Fadar Shugaban Najeriya da Majalisar Dokokin kasar saboda yinkurin canza jadawalin zabe da Majalisar ke yi, a yayin da shi kuma Shugaba Buhari ke son a bar shi yadda ya ke.
'Yan kwanaki kadan kawai bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar kaddamar da ayyukan cigaba da kuma jaddada zaman lafiya a jahar Filato, sai gashi kuma an yi jina-jina a Karamar Hukumar Bassa.
An yi wani babban rashi a fagen ilimin kimiyya, mumamman ma a bangaren nazarin duniyoyi, sanadiyyar rasuwar shahararren masanin kimiyya Stephen Hawking.
A wani al'amari da zai kara ma 'yan jam'iyyar Dimokarat gwiwa, tankarar Majalisar Dokokinsu na Pensylvania, ya kama hanyar doke na Republican.
Domin Kari