Yau ma mun samo ma ku amsoshin tambayoyi masu kayatarwa kan yadda ake fama da ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya alhalin kuwa ana matukar fari a wasu sassan. Akwai kuma kashi na biyu na amsar tambaya kan Hausawan Sudan.
Kamar yadda mu ka saba, yau ma mu na dauke da amsoshin tambayoyi masu masu kayatarwa: Yadda Turawan mulkin mallaka su ka shigo Najeriya da kuma bambancin Hausawan Sudan da na Najeriya.
Yau za a ji amsoshin tambayoyi kan wata mai dinbin tasiri a duniya, wato marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth II, wadda ta ga zamanai da dama ta kuma yi hulda da masarautu da hukumomi da Shugabannin kasashe da dama.
Sanin yanayin guguwa na da muhimmanci wajen banbanta sha-ci-fadi da kuma abin da ke na hakika. Don haka shi ma kashi na biyun na amsoshin tambaya kan guguwa, muhimmi ne.
Kamar yadda mu ka saba, yau ma mun kawo ma ku wani shiri mai kayatarwa, mai cike da bayanai game da yanayin guguwa.
Yau za a ji amsoshin tambayoyi kan takardar kudin CFA, kasashe masu amfani da harshen Faransanci da kuma musabbabin ambaliyar ruwa.
Wannan ne kashi na biyu kuma na karshe na amsar tambayar nan kan musabbabin yawan gobara a dazukan kasashen Yammacin duniya ko da kuwa ganyaye da ciyayi danyu ne sharab.
Yau za a ji bayani dalla dalla daga wani kwararren farfesa kan musabbabin yawan wutar daji a nahiyar Turai duk da sanyinta, sabanin Afurka, mai yawan yanayin zafi.
Yau za a ji kashi na hudu kuma na karshe na amsoshin tambayoyi kan shugabancin matasa a kasashen duniya.
Yau za a ji amsar tambayoyi kan man jirgin sama da kuma kashi na biyu na amsar tambaya game da shugabannin kasa matasa da tasirin shugabancinsu.
Yau dai za a ji bayani kan kasar da ta fi sanyi a duniya, da kuma maimaicin amsoshin tambayoyi kan kwamrad (comrade).
Wannan satin za a ji amsoshin tambayoyi ne kan dan gwagwarmaya da ake kira comrade (kwamrad) da kuma tarihin shahararren mawakin Hausa, Sani Dan Indo, kamar yadda wadanda su ka sani su ba bayyana.
• A ina Majalisar Dinkin Duniya ta ke? • Mene ne dalilin saka ma ta suna Majalisar Dinkin Duniya? • Wace irin gudunmawa majalisar ke bayarwa? • Majalisar na iya magana a yi aiki da maganar? A biyo mu, a ji cikakken bayani:
Tun bayan da aka fara yaki tsakanin Rasha, kasar da ta fi kowacce yawan makamin nukiliya a duniya, da Ukraine, wacce ke samun goyon bayan manyan kasashen Yamma wadanda wasunsu ke da makaman na nukiliya, aka yawaita tambayoyi kan nukliya.
Yau za a ji karshen tambayoyi kan abubuwan da su ka shafi azumi; musamman ma Zakkat ul Fitr, da kuma ranar Sallah.
Masu sauraronmu da dama sun yi tambayoyi iri iri kan Azumi. Yau mun gabatar ma ku da kashi na farko. Ranar Asabar mai zuwa za a ji kashi na biyu na bayanan da Sheikh Muhammad Ibrahim Duguri ya yi.
A wannan maimaicin Amsoshin Tambayoyinku, za a ji tarihin marigari Grema Boukar, mamallakin gidajen Rediyo da Talabijin na AMFANI a Jamhuriyar Nijer, da kuma tarihin Lord Lugard, wanda ya taka rawa wajen hada kudanci da arewacin Najeriya.
Tun bayan da aka kai harin da safiyar yau Talata ake ta jiran cikakken bayanin halin da ake ciki, ganin cewa da farko an ce akwai bama bamai. To amma daga bisani hankula sun dan kwanta bayan da aka ce babu wanda ya mutu zuwa yanzu. Amma daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, biyar na fama.
Domin Kari