Kungiyoyi da daidaikun jama'a na cigaba da gudanar da zanga-zanga a ciki da wajen Nijeriya na neman a sako 'yan matan da aka sace a makarantar Chibo da ke jihar Borno.
A wani al'amari mai nuna dan'uwantaka tsakanin matasan kasa da kasa, a Sudan daliban Jami'a sun yi zanga-zangar neman a maido da dalibai matan da aka sace a garin Chibok na Jihar Borno
Kowace ranar Allah takaicin iyayen dalibai matan da aka sace a Chibok sai karuwa ya ke yi saboda rashin sanin halin da 'ya'yansu ke ciki da kuma jita-jita daban-daban da su ke ta ji.
Yayin da aka share makonni uku da sace dalibai mata a makarantar Sakandare dake Cibok a Jihar Borno, wani dan Majalisar Wakilai ya tabbatar cewa 'yan bindigar sun fara auren 'yan matan.
An kai wasu jerin hare-hare da jefa bama-bamai akan kolejin 'yan shi'a a birnin Baghazada kasar Iraqi
A wajen jarabawar zabar kwararru da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta shirya mutane ashirin suka rasa rayukansu sanadiyar turereniya da sukayi.
Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta ko INEC a takaice ta fitar da jadawalin zaben 2015 wanda yanzu ya sa 'yan siyasa na ta yin tsokaci kan dacewar shirin ko rashin dacewa.
Jam'iyyar APC a jihar Sokoto ta fada cikin rikicin bangaranci sanadiyyar shiga Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko cikin jam'iyyar.
Ana nan ana kan shagulgulan cikar Nijar shekaru 55 da zama Janhuriya. Wannan ya biyo bayan wani jawabin da Shugaban kasa Isuhu Muhammadu ya yi, wanda ya tayar da kura daga bangaren 'yan adawa
A wani yinkuri na kyautata ma miskinai a jihar Borno, a karon farko gwamanatin jihar ta nada wani miskini a babban matsayi.
Wasu 'yan Janhuriyar Nijar sun sami kansu cikin tsaka mai wuya dangane da rikicin kabilanci da addinin da ke faruwa a Janhuriyar Afirka ta Tsakiya
Har yanzu bangarorin jam'iyyar CDS Rahama na jayayya kan batun babban taron sake zaben shugabanni ko "Congre."
Nakasassun jihar Bauchi sun ce gwamnatin jihar ta dau matakan kau da bara da su ka hada da samar ma su da abinci da koya masu sana'o'i.
Yayin da wa'adin yin babban taron "congre" da Ministan Cikin Gidan Janhuriyar Nijar ya bai wa jam'iyyar CDS ke cika, Shugaban Jam'iyyar Mallam Mahammadu Usumane ya ce Ministan bai da hurumi
Hukumomi a jihar Borno na arewa maso gabashin Nijeriya sun rage dokar hana fita kuma tuni ma aka maido da sadarwar waya a wasu wurare ne jiahr.
Kasashen Afirka na cigaba da jagoranci a fagen cin hanci da rashawa a duniya.
Gwamnatin Nijeriya ta himmantu ga taimaka ma yankin arewa maso gabashin Nijeriya a gwagwarmayarta yaki da fatara da ta'addanci, in ji Shugaba Goodluck Jonathan.
A wani yinkuri na farfado da tattalin arzikin arewa maso gabashin Nijeriya da ke tangal-tangal, za a yi wani babban taron tallata wuraren saka jari da ke jihohi shida na yankin a garin Gombe ranar Talata.
Attajirin nan da ke jihar Borno mai suna Mohammed Indimi ya sha alwashin kafa wani katafaren kamfanin samar da wutar lantarki a jihar Borno don kawo karshen durkushewar masana'antu sanadiyyar rashin wutar lantarki
Ana kan haramar gagarumin yaki da cutar kanjamau a gobe Lahadi, ita ce zagayowar ranar jaddada yaki da cutar da kuma kulawa da masu dauke da cutar.
Domin Kari