Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyayen Cibok Sun Yi Zanga-zanga a Borno


Gretsiyadagi muhojirlar

Kungiyoyi da daidaikun jama'a na cigaba da gudanar da zanga-zanga a ciki da wajen Nijeriya na neman a sako 'yan matan da aka sace a makarantar Chibo da ke jihar Borno.

Sama da makwanni biyu bayan ‘yan bindigar Boko Haram sun sace ‘yan mata dalibai daga gidan kwanansu a arewa maso gabashin Nijeriya, dangogin ‘yan matan da aka sace sun hadu jiya Alhamis a garin Chibok don yin zanga-zanga kan abin da su ka kira halin ko-oho na hukumomi da jami’an tsaron da aka dora ma nauyin neman yaran.

Daruruwan ‘yan’uwa yaran sun hadu a harabar makarantar sakandaren da aka kona, su na ta kuka mai zafi.

“Me ke faruwa, babu wanda ya damu, kuma gashi mu na ta kuka,” a ta bakin wani mutum wanda diyarsa ke cikin ‘yanmata 180 da har yansu ba a san inda su ke ba, tun bayan da aka sace su da karfin bindiga ran 14 ga watan Afrilu.

“Kuka mu ke ga daukacin mutanen duniya su taimaka, su agaza ma na.”

“Na rantse ma ka, ba su taba tuntubar kowa ba,” a cewa Aba, wani dan’uwar wata daga cikin ‘yan matan da aka sace. Ya na mai kira ga gwamnatin tarayya ko sojoji su rinka magana kai tsaye ga iyalan da abin ya shafa.

“Ba su taba yin bayani ma kowa ba in banda gwamnan jihar da ya zo nan bisa radin kansa, ya na kira ga iyaye da su yi hakuri ba da dadewa ba za a maido masu da ‘ya’yansu,” a cewar Aba. “Jami’an tsaro, ba su tabuka komai ba. Ba su yi komai ba. Sun zauna kawai wuri guda su ka nade hannayensu, ba su komai, ba su kuma cewa komai,”

Wannan ya zo daidai da bukatar wasu masu zanga-zangar da su ka yi maci bisa titunan Abuja cikin ruwa ranar Laraba, da su ka hada da ‘yan’uwan wadanda aka sace din, su na ta kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya da ta nemi taimakon kasa da kasa wajen fafatawarta da wannan kungiya mai tsattsaurar ra’ayin Islama, wanda wannan bukata ta neman taimakon kasa da kasa gwamnati na jan kafa a kai.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar kuma sun daga murya su na cewa, “Ku kawo ma na ‘yanmatan nan da rai! Abin da mu ke cewa kawai shi ne a kawo ma na yaranmu ‘yanmata,” a cewar wadanda su ka yi maci kwana guda da ta gabata a babban birnin kasar, inda su ka bukaci gwamnati ta dau kwararn matakan ceto ‘yan matan

Ana zargin kungiyar ta Boko Haram da maida ‘yan matan da su kan sace din ma’aikatansu, da masu leko masu asiri da kuma matan aurensu. Ana kuma kyautata zaton cewa ‘yan bindigar, wadanda fafatukarsu ta tsawon shekaru biyar ta yi sanadin mutuwar dubban mutane, sun kakkasa ‘yan matan da su ka sace su ka kai su sansanoninsu da dama da ke dajin Sambisa da ke kusa da kan iyakokin Nijeriya da Kamaru da kuma Chadi.

Kwanan nan wani jami’in leken asiri na Nijeriya da ke jihar Borno, ya gaya ma Muryar Amurka cewa hukumomi na kan binciken gano ko a wanne ne daga cikin mabuyun ‘yan bindigar da ke dajin Sambisa aka garkame ‘yan matan.

Duk kuwa da shafe sama da shekara guda da sojoji ke fafatawa da Boko Haram, jami’an tsaron Nijeriya sun kasa tsaida tashin hankalin da akan yi kusan kulluyaumin a kasar, musamman ma a arewa maso gabashin kasar. Yanzu kuma halin da ‘yan matan Chibok ke ciki ya zama wani al’amarin da ya shafi al’ummar kasar baki daya, wadanda ke takaicin gazawar gwamntin Nijeriya da ke Abuja wajen dakile wadannan abokan gaban da ke labe.

Labarai masu alaka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG