Sanatan mai wakiltar arewacin Borno, ciki har da garin Baga, yayi ikirarin cewa mutane akalla 228 ne suka mutu a wannan tashin hankali na makon jiya
‘Yan sanda a Bangladesh sun ce sun kama mai ginin rukunin kamfanonin nan da ya ruguje makon jiya, ya hallaka mutane sama da 350
Jami’an gwamnatin Aljeriya sun ce Shugaba Abdelaziz Bouteflika ya sami, abin da su ka kira, wani dan bugun zuciya, kuma ya na kan jinya a kasar Faransa.
Kasar Habasha ta zama ta farko da ta sake amfani jirgin sama samfurin Boeing 787 Dreamliner, bayan da aka datakar da amfani da rukunin wannan jirgi guda 50 a duniya watanni uku da su ka gabata
‘Yan sanda a Bangladesh sun kama mutane biyu masu masakar nan da ta ruguje kwanaki uku da su ka gabata, har daruruwan mutane su ka mutu.
Dubun dubatan masu goyon bayan Shugaban Masar Mohammed Morsi na gangami a harabar Jami’ar al-Khahira.
Babban kwamandan mayakan kungiyar ‘yan tawayen Congo mai suna M23 ya ce dakarunsa sun fara ficewa daga garin Masisi
An shiga rana ta 3 a zanga-zangar da ake yi a Masar kan shawarar da Shugaba Mohammed Morsi ya yanke ta kara wa kansa dinbin iko
Yan agaji a Bangladesh na kokarin gano gawarwakin mutane a kalla 112,
Firayim Ministan Isira’la Benjamin Netanyahu ya ce a shirye Isira’ila ta ke ta yi gagarimin fadada matakan da ta ke daukawa kan mayakan zirin Gaza
Kungiyar Tarayyar Afirka ta amince da shirin kai daukin soja, don taimakawa a fatattaki ‘yan bindigar Islama daga arewacin Mali.
Yau, 11 ga watan nan na Nuwamba, ta ke Ranar Tunawa da Mazan jiya a nan Amurka
An kashe Gwamnar Babban Bankin kasar Guinea.
Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana yau 10 ga watan Nuwamba a matsayin Ranar Malala
An bayyana Shugaban Amurka Barack Obama a matsayin wanda ya ci zaben jihar Florida inda aka fi yin kare-jini biri-jini, kwanaki hudu bayan da ya sake yin nasara a zaben Shugaban kasa.
China ta caccaki Majalisar Dinkin Duniya, saboda sukar ta da ta yi, kan yadda ta murkushe tashin hankalin da aka yi a yankunan Tibet
Fafatawa mai zafi, wadda kuma aka dau lokaci mai tsawo ana yi, ta neman zama Shugaban Amurka na shekaru hudu daga yanzu, ta zo karshe a yayin da ‘yan takarar biyu da kowannensu ke da tasiri
Tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton ya kasance a tawagar yakin neman zabe da Shugaba Barack Obama da daren jiya Asabar
Jami’ai a gabashin Kenya sun ce wani harin gurnatin da aka kai kan wata Majami’a yau Lahadi, ya raunata akalla mutane 8, wasu da tsanani sosai.
Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Amnesty Int’l, ta ce matakan da jami’an tsaron Nijeriya ke daukawa game da kungiyar Boko Haram na dada yamutsa al’amura.
Domin Kari